Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Thursday, March 5, 2020

  Tirkashi: Saurayi ya yiwa budurwarshi tsirara a cikin jama'a saboda taki yadda ta aure shi
  - Wani bidiyon masoya biyu da lamarin soyayyarsu ya watse ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani - A bidiyon dai an ga saurayin ya durkusa kasa yana neman amincewar budurwa shi don aurenshi a cikin wani wajen cin abinci mai cike da jama’a 


  - Bayan kin amincewarta ne ya tashi a fusace inda ya juye abincin da ya siya mata a leda tare da kwace takalmin da ke kafarta don ya ce shi ya siya Ka kwatanta yadda za ka ji idan mace ta nuna rashin son ka fili kuma cikin bainar jama’a. A yayin da kayi kokarin bayyana mata burinka na aurenta a wajen cin abincin da ke cike da mutane amma ta ki aminta da kudirinka. 

  Wani abin kunya da bada haushi ne ya faru da wani matashi wanda ya bukaci budurwar shi ta aure shi a gaban jama’a amma ta nuna bata amince ba. Tuni fusataccen saurayin ya tube mata takalman da ke kafarta don a cewar shi, shi ya siyo su. 


  Kafin cire mata takalman, fusataccen matashin sai da ya fara juye abincin da ya siya mata a cikin leda baka. Bayan ya karbe kayayyakin shi, sai ya fice daga wajen cin abincin a fusace, kamar yadda jaridar Pulse.ng ta wallafa. 

  Kamar yadda bidiyon ya nuna, an gano cewa saurayin da budurwar sun dade suna soyayya amma sai saurayin yayi tunanin ya kamata su kai wani mataki a soyayyar. Bai kuma taba tsammanin cewa budurwar na da wani tunanin da ba hakan ba. Budurwar kuwa ta sha mamaki da yadda saurayin nata ya yi martanin abinda tayi mishi, don kuwa ta kasa cewa komai balle ta iya tashi daga kujerar da take. Tuni dai bidiyon masoyan biyu ya yi yawa a yanar gizo kuma mutane daban-daban na ta yin tsokaci a kan hakan.

  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Tirkashi: Saurayi ya yiwa budurwarshi tsirara a cikin jama'a saboda taki yadda ta aure shi Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI