--
IGP ya bayyana su waye 'yan bindigan yankin Arewa maso Yamma

IGP ya bayyana su waye 'yan bindigan yankin Arewa maso Yamma

Sifeta Janar din ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ce ‘yan bindigar da ke aika-aika a yankin Arewa maso Yamma din kasar nan duk mayakan Boko Haram ne da ISWAP. A yayin magana a ranar Laraba yayin taro da manyan kwamandojin ‘yan sanda a kan harin kwanan nan da aka kai jihar Kaduna, Sifeta Janar ya ce sabbbin hare-haren da ake kawowa suna bukatar sabbin salon yaki don batar da ‘yan bindigar daga maboyarsu. 

Shugaban ‘yan sandan ya kara da cewa, akwai tsananin amfani idan aka tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan. Ya ce, “Na yanke shawarar zuwa Kaduna ne don tattaunawa da manyan jami’an da kuma sanin sabbin salon yaki da ta’addanci da suke shirayawa. Saboda munsan dai akwai alamun Boko haram a ciki da kewayen jihar kuma hakan ne yasa dole mu zage damtse don batar da su.” “Shiyasa a ranar 5 ga watan Fabrairun 2020 muka ziyarci dajin da ‘yan bindigar suke. A ranar 21 ga watan Fabrairun ne muka samu shiga sansanin ‘yan bindigar inda muka tarwatsasu da hadin guiwar wata cibiyar tsaro. Wannan dabarar zamu ci gaba da amfani da ita wajen kawo karshen ta’addanci, in ji shi. 

IGP ya bayyana su waye 'yan bindigan yankin Arewa maso gabas Source: Twitter 

“Babu gudu kuma babu ja da baya. Abinda ya faru ba zai sake faruwa ba don ba zamu bari ba. Na samu labarin abinda ya kawo wannan harin ga kauyukan,” ya kara da cewa. Ya yi kira ga jama’a da su ba ‘yan sandan hadin kai wajen samar da gamsassun bayanai don shawo kan matsalar tsaro. Ya kara da jawo hankulan ‘yan sandan da su dage wajen zuwa har sansanin ‘yan ta’addan don tarwatsa su. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sifeta janar din ‘yan sandan Najeriya, ya zamu ganawa da jami’an tsaro bayan harin ranar Lahadi da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyukan jihar a ranar Lahadi. Harin yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane 51 a kauyukan kananan hukumomin Igabi da Giwa na jihar Kaduna din.LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 



0 Response to "IGP ya bayyana su waye 'yan bindigan yankin Arewa maso Yamma"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?