--
A dinga barin mata suna auren maza biyu ko da za a samu akasi daya ya mutu - Jarumar fim

A dinga barin mata suna auren maza biyu ko da za a samu akasi daya ya mutu - Jarumar fim

- Wata jaruma a masana’antar Nolywood mai suna Susan Peters ta wallafa wani sako da ya jawo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani - Susan Peter dai ta bukaci a amincewa mata ne su fara auren maza fiye da daya a duniyar nan - A hikima irin ta ta kuwa, ta ce hakan zai zamo kamar tallafi ga matan idan miji daya ya rasu Wata jarumar masana’antar Nollywood mai suna Susan Peters ta wallafa wani sako da ya jawo cece-kuce a shafinta na kafar sada zumuntar zamani. Peters dai ta wallafa sakon ne kuma mutane suka dinga caccakarta. Mahaifiyar mutum daya din, 

ta ce me zai hana mata a barsu su dinga auren maza fiye da daya suma. Ta ce ya kamata yayi a bar hakan tana faruwa ta yadda mata za su iya samun madogara koda kuwa bayan mutuwar miji daya ne daga ciki, kamar yadda Information.ng ta ruwaito. 


Peter dai ta taba auren wani likita dan asalin kasar Holland mai suna Dr Croon. Sun yi auren ne a 2015 amma babu dadewa suka rabu. A wani bangare na daban kuwa, Legit.ng ta ruwaito cewa Zancen auren mace fiye da daya har yanzu yana jawo cece-kuce daga bangarori da dama na Najeriya. Daga tsokacin da ake samu kuwa, mata na ci gaba da sukar auren mace fiye da daya. 

Wasu mata ko maza da suke sukar auren mace fiye da dayan na kafa hujjoji ne daga mahangar addinin Kirista. Amma kuma abu daya ne wanda kowa ya san shi, shine mata sun fi maza yawa. Idan kuwa aka dubi hakan, wa zai auri matan da basu riga sun yi aure ba? Wani abu da ake mantawa kuwa shine, ba kowanne namiji bane yake iya zama da mace daya ba.

Hakazalika, namiji mai shekaru 100 zai iya yi wa mace ciki amma matan masu shekaru da yawa basu iya dauka. Wannan lamarin kuwa yasa maza suke fadawa neman matan banza koda kuwa suna da aure. 

A yayin da yawaitar zawarawa da kuma neman mata yake ci gaba, wata mata ta shawarci mata a kan mazansu masu yunkurin auren mata su kawo gidansu. Ta bukaci matan da su saka ransu a cikin salama tare da yarjewa mazansu auren wasu matan. Ta ce: "Yan uwana maza, ku auri mata a maimakon ku dinga neman mata bayan kuna da aure." Tayi kira ga maza a kan su ji tsoron Allah kuma su auri mace fiye da daya. Ta kammala da cewa "ku ji tsoron Ubangiji ku auri mata."


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 



0 Response to "A dinga barin mata suna auren maza biyu ko da za a samu akasi daya ya mutu - Jarumar fim"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?