--
Yanzu-yanzu: An haramta bara a jihar Neja

Yanzu-yanzu: An haramta bara a jihar Neja

Gwamnatin jihar Neja karkashin jagoraninc gwamna Abubakar Sani Bello, ta haramta kowani irin bara a titi a fadin jihar saboda dalilai na tsaro. Kwamishanan yada labaran jihar, Mohammed Idris, 

ya bayyana hakan ne a hira da yayi da manema labarai a Minna, inda yace abinda majalisar zantarwar jihar ta zartar kenan a ganawarta na mako-mako. Ya ce wannan doka za ta fara aiki ne daga ranar 5 ga Maris, saboda rahotanni daga hukumomin tsaro ya tilastawa gwamnatin jihar daukan mataki mai tsauri kan bara da mabarata. 

“An yi hakan ne saboda akwai lamarin rashin tsaro dake karuwa kullun a jihar, saboda haka haramta bara zai taimaka wajen rage wadannan kalubale.,” 

Yace Idris ya ce an dau wannan mataki ne domin kare rayuka da dukiyan mazauna jihar kuma za a tsaurara matakai kan wadannan sukayi kunnen kashi. Ya kara da cewa, za a damke duk wani babba da aka kama yana bara, kuma a hukunta iyayen yaran da aka kama suna bara a titi. 

Yanzu-yanzu: An haramta bara a jihar Neja Source: Depositphotos 

Shahrarren masanin addinin Islama, Dakta Mansur Ibrahim Sokoto, ya yabawa gwamnatocin jihar Kano da Nasarawa kan haramta bara ga Almajirai. Malamin ya bayyana cewa can dama babu wata alaka tsakanin bara da almajiranci.

 ya yi kira ga gwamnonin sun fito da wasu hanyoyin rage talauci da yunwa cikin masu aikin barace-barace. A cewarsa: “Bara daban, almajirci daban. Matakin da jihohin Kano da Nasarawa suka dauka abin yabawa ne, da sharadin a fito da karfafan hanyoyin rage radadin talauci.“ 

Mun kawo muku rahoton cewa gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya haramta bara a titunan jihar. Ya sanar da hakan ne yayin rantsar da hukumar kare hakkin yara a Lafia a ranar Laraba. Hakazalika gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Talata ya alanta dokar haramta bara ga almajirai a jihar. 


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Yanzu-yanzu: An haramta bara a jihar Neja"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?