--
Da duminsa: Kotu a Kano ta jingine hukuncin dakatar da Oshiomhole a gefe

Da duminsa: Kotu a Kano ta jingine hukuncin dakatar da Oshiomhole a gefe


Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke jihar Kano ta jingine hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja na dakatar da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adam Oshiomhole, a ranar Laraba. A hukuncin da kotun ta yanke ranar Alhamis, 

mai shari'a, Jastis Lewis Allagoa, ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da rundunar 'yan sanda (NPF) a kan su mayar wa da Oshiomhole jami'an da ke tsaron lafiyarsa domin ya koma ofishinsa. A ranar Labara ne mai shari'a, Jastis Danlami Senchi, ya bayar umarnin wucin gadi na dakatar da Oshiomhole daga gabatar da kansa a matsayin shugaban APC na kasa.

Oshiomhole Source: Depositphotos 


Sa'o'i kadan bayan zartar da hukuncin kotun a ranar Laraba, Oshiomhole ya daukaka kara zuwa wata kotun daukaka 



Rahotanni sun bayyana cewa mai shari'a, Jastis Lewis Allagoa, ne ya yanke hukuncin jingine dakatarwar da aka yi wa Oshiomhole ranar Laraba. Sai dai, har yanzu ba a samu cikakken rahoto a kan waye ya shigar da kara a kotun Kano dangane da dakatar da Oshiomhole ba. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Da duminsa: Kotu a Kano ta jingine hukuncin dakatar da Oshiomhole a gefe"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?