--
Sabbin mutum 5 sun kamu da coronavirus, ta shiga karin sabbin jihohi 2

Sabbin mutum 5 sun kamu da coronavirus, ta shiga karin sabbin jihohi 2

An samu karin sabbin mutane biyar sun kamu da kwayar cutar coronavirus a Najeriya: biyu a jihar Legas, biyu a Abuja, da kuma mutum daya daga jihar Ribas. 

A sanarwar da ta fitar a shafinta na tuwita da daren ranar Laraba, cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa uku daga cikin mutanen matafiya da suka dawo Najeriya yayin da mutane biyu sun kamu da kwayar cutar ne sakamakon cudanya da masu dauke da kwayar cutar. 




 Ya zuwa yanzu jimillar masu dauke da kwayar cutar a Najeriya ya koma mutum 51 a jihohin Najeriya 9. 

Hakan ya nuna cewa kwayar cutar coronavirus ta shiga jihohin Osun da Ribas a karon Farko:


 Ya zuwa yanzu kwayar cutar coronavirus ta hallaka mutane 15,000 a fadin duniya. Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, sannan an sallami mutane biyu da suka warke bayan sun sha magungun a cibiyar da aka killace su, 

kamar yadda kididdigar NCDC ta nuna. Yawacin mutanen da aka samu da kwayar cutar corona a Najeriya, 'yan kasa ne da suka dawo daga kasashen ketare, musamman turai. An tabbatar da samun kwayar cutar a jikin manyan jami'an gwamnati guda uku. 

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, shine na farko da aka fara tabbatarwa yana dauke da kwayar cutar. Na biyu shine gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed,

sai kuma kakakin majalisar jihar Edo. Ya zuwa yanzu, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da wasu gwamnoni da manyan jami'an gwamnati sun killace kansu bayan sun gano cewa sun yi mu'amala da masu dauke da kwayar cutar. 

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Sabbin mutum 5 sun kamu da coronavirus, ta shiga karin sabbin jihohi 2 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?