MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"

Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Wednesday, March 25, 2020

  Rashin iya gamsar da matarsa a wurin kwanciya ya saka wani mutum kashe kansa  Wani mai gyaran kayayyakin wutar lantarki, Victor Edem ya kashe kansa saboda matsalar da ya fama da ita na gaza gamsar da matarsa yayin kwanciya da kuma gaza yi mata ciki. 

  An tsinci gawar Mista Edem, mazaunin garin Okpanam kusa a Asaba a jihar Delta a daren ranar Litinin a cikin dakinsa inda a baya ya ke zaune da matarsa da dansa kafin su rabu a shekarar bara saboda matsaloli masu dangantaka da rashin karfin mazakuta. A cewar wata majiya, 


  Mista Edem wanda dan asalin garin Calabar ne a jihar Cross Rivers ya sanar da daya daga cikin abokansa game da matsalar da ya ke fama da ita kuma ya yi barazanar zai kashe kansa idan bai samu maganin ta ba. 

  An kuma gano cewa Mista Edem ya dade yana kashe makuden kudi domin magance matsalar amma daga bisani ya shiga cikin damuwa da kuma kashe kansa.   Wani mazaunin unguwar da Mista Edem ya ke da ya yi magana kuma ya nemi a sakayya sunansa ya ce tsohuwar matar na mutumin da wahal da shi sosai sakamakon matsalar da ya ke fama da ita kafin daga bisani ta kwashe kayanta ta bar gidansa. A cewar mazaunin unguwar, 

  bisa ga dukkan alamu mazakutar Mista Edem ta dena aiki duba da cewa ya kasa zama da mace a gidansa cikin dan lokacin da ya yi ta kawo wasu matan. Kwamishinan 'yan sandan jihar, Hafiz Inuwah ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce babu tabbas cewa mutumin ne ya kashe kansa duba da cewa babu wata wasika da ya rubuta ya bari na bayanin dalilin da yasa ya kashe kansa. 


  Amma Mista Inuwa ya ce an ga wasu lambobin waya guda biyu a dakin da aka tsinci gawar Mista Edem tana sagale da igiya daga rufin dakin. Daya daga cikin manyan unguwar, Ogbueshi Osakwe wanda ya yi magana da manema labarai ya ce Mista Edem ya tafka babban laifi na kashe kansa saboda rashin karfin mazakuta inda ya ce zai fuskanci hukunci a lahira kan abinda ya aikata.LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Rashin iya gamsar da matarsa a wurin kwanciya ya saka wani mutum kashe kansa Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI