--
Ba shiga ba fita: Ganduje ya kulle jahar Kano gaba daya saboda tsoron Coronavirus

Ba shiga ba fita: Ganduje ya kulle jahar Kano gaba daya saboda tsoron Coronavirus

Gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da shirinta na garkame jahar Kano gaba daya ta hanyar rufe duk wata hanya da ta shiga jahar daga sauran makwabta jahohi. 

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne a kokarin na yaki da yaduwar mugunyar cutar nan mai toshe numfashi, watau annobar Coronavirus, kamar yadda hadimin gwamnan na musamman a kan harkokin kafafen watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana. 

Yakasai ya ce: “Mai girma gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin rufe duk wata hanya da ta shiga jahar Kano, hatta filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano, farawa daga tsakar daren Juma’a. 

“Babu wanda za’a bari ya shiga ko ya fita daga jahar Kano daga tsakar daren Juma’a, 27 ga watan Maris. Don haka duk masu son shiga Kano ko fita daga Kano, su gaggauta yin haka kafin tsakar daren Juma’a.” 

"Inji shi. Sanarwar ta karkare da cewa har yanzu babu wanda aka samu dauke da kwayar cutar a jahar Kano, amma dai an dauki wannan mataki ne a matsayin rigakafi tare da kare yaduwar cutar daga wasu jahohi zuwa jahar. 

A wani labarin kuma, fadar gwamnatin jahar Nassarawa ta fitara da sanarwa game da sakamakon gwajin da jami’an hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta gudanar a kan gwamnan jahar, Abdullahi Sule. Legit.ng ta ruwaito sanarwar ta tabbatar ma al’ummar jahar Nassarawa, yan uwa da abokan arzikin gwamnan da ma sauran jama’an Najeriya cewa gwamnan ya sha,


duba da cewa sakamakon gwajin ya nuna baya dauke da kwayar cutar Coronavirus mai toshe numfashi. Sai dai duk da wannan tabbaci da sakamakon gwajin ya nuna, Gwamna Abdullahi Sule ya dauki matain killace kansa tare da cigaba da gudanar da aiki daga gida domin ya rage cudanya da jama’a, don gudun kada kuma ya kamu. 

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Ba shiga ba fita: Ganduje ya kulle jahar Kano gaba daya saboda tsoron Coronavirus "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?