Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com "Colour"
 • LABARAN YAU

  Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki,

  ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________
  Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views

  Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Thursday, March 26, 2020

  Coronavirus ta sa wata tsohuwa 'Yar Kano ta yi shahada a Amurka

  - Allah ya yiwa wata ‘yar asalin jahar Kano da ke zama a Amurka mai suna, Hajia Laila Abubakar Ali rasuwa - Tsohuwar mai shekara 60 ta rasu ne bayan ta kamu da cutar coronavirus

  - Ta kasance yayar sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin addini na Kano Rahotanni da ke zuwa mana ya nuna cewar Allah ya yiwa wata ‘yar asalin jahar Kano da ke zama a Amurka mai suna, Hajia Laila Abubakar Ali rasuwa. Tsohuwar mai shekara 60 ta rasu ne bayan ta kamu da cutar coronavirus. Kakakin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano, Salihu Yakasai ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris.

  A wani rubutu da ya wallafa a twitter, ya bayyana cewar marigayiyar ta kasance yayar sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin addini na Kano.

  Ya wallafa: “Wata ‘yar asalin Kano da ke zama Amurka mai suna Hajia Laila Abubakar Ali ta mutu sakamakon cutar Covid-19. Tsohuwar mai shekara 60 ta mutu a jiya bayan ta kamu. Ta kasance yayar sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin addini na Kano. Allah ya ji kanta da rahma.”   A bangare guda mun ji cewa an rufe majalisar wakilan tarayya da kuma ta dattawa a Najeriya, a sakamakon cutar Coronavirus da ta shigo Najeriya, har ta yi sanadiyyar mutuwar wani. A Ranar 25 ga Watan Maris, Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa an rufe majalisun tarayyar domin a hana yaduwar cutar COVID-19 da ta shiga kasashe fiye da 190. Shugaban majalisar dattawa watau Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ya bada wannan sanarwa bayan wani zama da su ka yi na kusan sa’a guda a Ranar Talatar nan da ta gabata.

  Ahmad Lawan ya ce Sanatoci sun dakatar da aiki a majalisar, sai dai a cewarsa, za su tsaya jiran aikin ko-ta-kwana a Abuja, su dawo bakin aiki idan akwai bukatar gaggawa. Lawan ya ce Sanatocin za su tafi hutun makonni biyu, za su dawo bakin aiki a Ranar 7 ga Watan Afrilu. Lawan ya yi kira ga gwamnati ta dage wajen yakar wannan cuta.
  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Coronavirus ta sa wata tsohuwa 'Yar Kano ta yi shahada a Amurka Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI