--
Nayi bakin cikin kashe mutum daya, na so kashe dukkan makwabtana ne - Wanda ake zargi

Nayi bakin cikin kashe mutum daya, na so kashe dukkan makwabtana ne - Wanda ake zargi


- Wani matashi da ake zargi da kisan kai mai shekaru 27 mai suna Ejike Eze, ya bayyana rashin jin dadinsa na kasa kashe dukkan makwabtan shi - Dan asalin jihar Ebonyi din da ke zama a yankin Ayegbami da ke Ijebu Ode na jihar Ogun yana sana’ar kyadi ne tun bayan saukar shi a garin 

- Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ne suka damke Eze bayan an zarge shi da sokawa wata makwabciyar shi wuka bayan ta zarge shi da satar wayarta Wani matashi da ake zargi da kisan kai mai shekaru 27 mai suna Ejike Eze, ya bayyana rashin jin dadinsa na kasa kashe dukkan makwabtan shi a jihar Ogun. Dan asalin jihar Ebonyi din da ke zama a yankin Ayegbami da ke Ijebu Ode na jihar Ogun, yana sana’ar kyadi ne tun bayan saukar shi a garin. 

Gidan da yake zaune kuwa ya cika ne da ‘yan kabilar Yoruba da Igbo. Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ne suka damke Eze bayan an zarge shi da sokawa wata makwabciyar shi wuka bayan ta zarge shi da satar wayarta. Lamarin kuwa ya auku ne a ranar Juma’a da ta gabata. An gano cewa, Eze da matar da ta rasu mai shekaru 59 sam basu jituwa amma sai a ranar ta zarge shi da satar wayarta. Fusatar da ya yi da lamarin ne yasa ya kai mata hari inda ya kasheta tare da guduwa. Bayan kwanaki biyu kuwa sai ‘yan sanda suka damke shi a tashar motar Ijebu Ode yana shirin barin garin. 

A yayin da manema labarai suka bukaci jin ta bakin wanda ake zargin a hedkwatar ‘yan sandan da ke Eleweran, ya bayyana a fusace. An garkame shi ne a sashi na musamman na bincikar laifukan kisan kai don bincike tare da gurfanarwa. Ya zargi dukkan makwabtan shi da yaransu da zama makiyan shi kuma bai ji dadi ba da bai kashesu duka ba. “Ina garkame ne saboda kisan kai da nayi. Na soki makwabciyata ce wacce ba zan iya tuna sunanta ba. 

Muna zama a gida daya ne da ke yankin Ayegbami a Ijebu Ode a jihar Ogun. “Mamaciyar ta zargeni ne da satar mata waya. A duk lokacin da ta zargeni, sauran ‘yan hayar na goyon bayanta. Suna zagi na tare da min ihu,” jaridar The Punch ta ruwaito yana cewa. “A ranar juma’a da wajen karfe 5:30 na safe ne naji tana zagina da yarbanci. Ta zargeni da satar mata waya. Kawai sai na yanke hukuncin harar ta da adda. Na sara mata a kai amma sai wasu ‘yan gidan suka nemi kwatarta, suma kuwa sai na bi su da ita.” Ya ce.LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Nayi bakin cikin kashe mutum daya, na so kashe dukkan makwabtana ne - Wanda ake zargi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?