--
Sabon rikici ya barke tsakanin gwamnatin Kano, masarauta da Nasiru Bayero

Sabon rikici ya barke tsakanin gwamnatin Kano, masarauta da Nasiru Bayero



Sabon rikici ya kunno kai tsakanin gwamnatin Kano da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero a kan zargin ‘ka karba daga gareni kuma ka ci min dunduniya.’
Kamar yadda majiyoyi da dama suka gano, Dabo Fm ta ruwaito cewa Nasiru Ado bayero ya ki yarda da nadin da aka yi masa na sarkin Bichi bisa dalilai masu yawa.

Daga cikin dalilan kuwa akwai zargin cewa ya baiwa gwamnatin Kano da wasu masu nema masa Sarki harda uwargidan gwamnan Kano wasu kudade masu yawa, bayan anyi masa alkawarin za a bashi kujerar sarkin Kano ba ta Bichi ba.
Majiyar ta tabbatarwa da dabo Fm cewa Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero yayi ikirarin cewa yana da shaidun dukkanin kudaden da ya biya domin siyan sarautar gidan dabo.

A halin yanzu dai yana shaida cewa kodai a biya shi kudinsa da ya kashe ko kuma a mayar da Sarkin Kano Aminu Bayero Bichi shi kuwa ya komo sarautar Dabo.
Hakazalika, majiyar ta tabbatarwa da Dabo FM cewar akwai wasu shirye-shiryen da masarautar Kano takeyi na tube rawanin wasu hakimai da masu mukamai, ciki kuwa har da wazirin Kano.
Biyo bayan tsige wasu daga cikin manyan kujeru da suka hada da Makaman Kano da sarkin dawaki mai tuta da sauransu, an gano cewa sun ci gaba da zuwa masarautar Kano din domin dama basu yarda da sabbin masarautun ba, kuma Muhammadu Sanusi II ya ci gaba da biyansu kudaden da ake basu.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Sabon rikici ya barke tsakanin gwamnatin Kano, masarauta da Nasiru Bayero"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?