--
Na kama mijina 'turmi da tabarya' yana lalata da matar aure - Matar Liman

Na kama mijina 'turmi da tabarya' yana lalata da matar aure - Matar Liman

Wata mata, Rebecca Adeniyi, ta sanar da kotun gargajiya da ke zamanta a yankin Igando, jihar Legas, cewa ta kama mijinta turmi da tabarya yana lalata da matar aure. A cewar Rebecca, mjinta mai suna Yusuf ya gina Masallaci tare da mayar da shi wurin lalata da mata masu aure da marasa aure. 

"Na kama shi turmi da tabarya yana lalata da daya daga cikin matan auren da ke zuwa Masallacinsa. Na rike matar, na yaga mata tufafi. "Na so na kwarmata maganar kowa ya sani, amma sai ya fara rokona a kan na rufa wa matar asiri don kada mijinta ya sake ta. "Jama'a sun kaurace wa Masallacin saboda halayen mijina na banza, amma yanzu kuma ni yake zargi da korar mabiyansa. "Tun bayan lokacin da na kama shi ya sauya min, ya daina bani kulawa, ya daina bani kudin abinci," a cewar Rebecca, uwar 'ya'ya hudu.

Na kama mijina dumu-dumu yana lalata da matar aure - Matar Liman ta sanar da kotu Source: UGC 

Malamin addinin, mai shekaru 47 a duniya, ya amsa laifin cewa yana lalata da matan aure da ke zuwa Masallacinsa, sai dai, ya dora laifin yin hakan a kan sharrin shaidan. "Na roki mata ta a kan ta yafe min, na daukar mata alkawarin cewa ba zan kara ba, amma duk da haka sai da ta tona min asiri," a cewarsa. 

Liman Yusuf ya zargi matar tasa da yin lalata da mijin matar da ta kama shi yana lalata da ita a cikin Masallacinsa. "Yanzu haka matata tana zaune ne da mijin matar da ta kama mu tare," a cewar Liman Yusuf. Yusuf ya roki kotun a kan kar ta raba auren da ke tsakaninsa da matarsa, kamar yadda ta nema. Bayan kammala sauraron kowanne bangare, shugaban kotun, Mista Adeniyi Koledoye, ya tsayar da ranar 20 ga wata domin yanke hukunci. 

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Na kama mijina 'turmi da tabarya' yana lalata da matar aure - Matar Liman"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?