Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com "Colour"
 • LABARAN YAU

  Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki,

  ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________
  Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views

  Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Wednesday, March 4, 2020

  NDLEA ta kama carbi 1,360 na alburusai a kan hanyar Bauchi zuwa Jos (Hoto)

  Hukumar hana sha da yaki da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Bauchi ta yi nasarar kama carbi 1,360 na alburusai yayin faturu a kan babbar hanyar Bauchi zuwa Jos. Shugaban sashen hulda da jama'a na NDLEA, Jonah Achema, shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya aika wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NDLEA) ranar Laraba a Abuja. 

  Achema ya bayyana cewa sun kama alburusan ne a cikin wata motar fasinja kirar 'Vectra' a hanyarta ta zuwa Jos, babban birnin jihar Filato. "Yayin da muke tuhumar fasinjojin motar, wasu fasinjoji guda biyu sun amsa cewa alburusan; wadanda ke boye a cikin jakankun guda biyu a bayan motar, mallkarsu ne. "Sun dauko wannan kaya mai guba ne daga garin Numan, jihar Adamawa, kuma zasu kai wa wasu masu saya ne a jihar Filato. Masu laifin sun gaza nuna wata shaida da ta basu damar safarar alburusan.

  NDLEA ta kama carbi 1,360 na alburusai a kan hanyar Bauchi zuwa Jos Source: Twitter 

  Mista Achema ya ce masu laifin sun tabbatar musu da cewa suna sayar da kowanne alburushi a kan farashin N500.

  Daya daga cikin masu laifin ya bayyana cewa, "kasuwanci ne a wurin mu. Al'amura sun yi tsanani a kasar na, hakan yasa dole mu nemi duk wata hanya da za mu ciyar da iyalinmu." Kwamnadan NDLEA reshen jihar Bauchi, Segun Kolawole Oke, ya ce za su mika masu laifin da alburusan hannun rundunar 'yan sanda domin zurfafa bincike. A cewarsa, 

  "wurin da suka dauko alburusan da kuma inda zasu kai su, duk wurare ne da ke fama da rashin zaman lafiya sakamakon amfani da makamai ta hanyoyin da basu dace ba." "A saboda haka, ba zamu dauki maganar safarar makamai da wasa ba," a cewarsa. LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI   • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: NDLEA ta kama carbi 1,360 na alburusai a kan hanyar Bauchi zuwa Jos (Hoto) Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI