\ Yanzun-nan: APC ta ce za ta bi umurnin kotu kan Oshiomhole - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Yanzun-nan: APC ta ce za ta bi umurnin kotu kan Oshiomhole - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
 • LABARAN YAU

  Wednesday, March 4, 2020

  Yanzun-nan: APC ta ce za ta bi umurnin kotu kan Oshiomhole



  - Mukaddashin sakataren jam’iyyar APC na kasa, Cif Victor Giadom ya bayyana cewar jam’iyyar za ta mutunta umurnin kotu da ta dakatar da Adams Oshiomhole daga matsayin shugaban jam'iyyar - Wata babbar kotun birnin tarayya a ranar Laraba, 4 ga watan Maris, ta hana Oshiomhole daukar kansa a matsayin shugaban jam’iyyar -

  -Giadom ya fada wa manema labarai cewa jam’iyyar za ta bi umurnin Mukaddashin sakataren jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Cif Victor Giadom ya kaddamar da cewar jam’iyyar za ta mutunta umurnin kotu da ta dakatar da Shugaban ta na kasa, Adams Oshiomhole. Wata babbar kotun birnin tarayya a ranar Laraba, 4 ga watan Maris, ta hana Oshiomhole daukar kansa a matsayin shugaban jam’iyyar.


  Yanzun-nan: APC za ta bi umurnin kotu kan Oshiomhole Source: Depositphotos 

  Da yake martani ga hukuncin, Giadom ya fada wa manema labarai cewa jam’iyyar za ta bi umurnin.


  Mun dai ji cewa Mai shari’a Danlami Senchi a ranar Laraba, ya ba Oshiomhole umarnin ya daina kiran kansa da shugaban jam’iyyar ta kasa har sai lokacin da aka kammala shari’ar da ta ke bukatar tumbuke shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC din. 


  Kotun ta bada umarnin ne bayan ta samu korafi a ranar 16 ga Janairu na Mustapha Salihu, mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa maso gabas; Anselm Ojezua, shugaban jam’iyyar na jihar Oyo da wasu mutane hudu. Korafin anyi shi ne a kan Oshiomhole, jam’iyyar APC, sifeta janar din ‘yan sandan Najeriya da kuma hukumar tsaro ta fararen kaya (SSS).


  Ta hannun lauyansu, Oluwole Afolabi suka bukaci kotun da ta hana Oshiomhole bayyana kansa ko yin wasu aiyuka da zasu nuna shi a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa baki daya har sai lokacin da shari’ar ta kammala. Sun kara da bukatar kotun da ta hana Oshiomhole yanke wani hukunci a matsayin shugaban jam’iyyar APC din na kasa tare da hana shi shiga ofishinsa har sai an kammala shari’ar.LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 



  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Yanzun-nan: APC ta ce za ta bi umurnin kotu kan Oshiomhole Rating: 5 Reviewed By: Admin
  site-verification: 8b0db1c078bc0934ee385b3afb5129be