--
Majalisar Kano Za Ta Fara Sauraron Korafi Kan Sarki Sanusi

Majalisar Kano Za Ta Fara Sauraron Korafi Kan Sarki Sanusi

Ranar Laraba, Majalisar jihar Kano ta fara karbar korafi kan Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na II.
Wasu kungiyoyin fararen hula biyu sun kawo korafi kan Sarkin, wanda kuma Shugaban Kwamitin Majalisa kan kananan hukumomi da masarautun gargajiya, kuma dan majalisa mai wakiltar Gundumar Sumaila, Hamza Massu ya karanto a bainar jama’a.
Massu ya ce, korafi na farko daga Shugaban Society for the Promotion of Education and Culture, Muhammad Bello, ne sai kuma na biyu na dauke da sa hannun Mohammed Mukhtar Ja’in Yamma.
A cewar korafe-korafen, akwai bukatar a binciki basaraken kan ayyukan ko-in-kulan da yake yi, wanda a cewarsu hakan ya saba wa addini da al’adun mutanen Kano.
Ya kara da cewa: “Baya ga korafin akwai kuma faifan bidiyo guda biyu da suka kawo saboda kafa hujja kan batutuwan da suka kawo cikin korafin.
“Masu korafin suna son a binciki sarkin ne, a kuma dauki mataki a kansa.”
Mataimakin Shugaban Majalisar, Injiniya Hamisu Chidari, ya ba kwamitin mako daya ta kawo rahotonta.
An kara Shugaban masu rinjaye, Kabiru Hassan da Mai kula da da’a, Labaran Ayuba a matsayin sabbin mambobin da za su taimakawa kwamitin wajen binciken.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 



0 Response to "Majalisar Kano Za Ta Fara Sauraron Korafi Kan Sarki Sanusi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?