MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"
 • Latest News

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Wednesday, March 4, 2020

  Matasa sun yiwa budurwa 'yar madigo fyade domin su gyarata ta fara son maza  - Matasa sun yiwa wata budurwa 'yar madigo fyade a kasar Afrika ta Kudu, inda suka ce sunyi hakane don su daidaita ta ta fara son maza - Mazan guda uku sun kama budurwar a lokacin da take kan hanyarta ta zuwa wani shago - Jami'an tsaro sun samu damar cafke biyu daga cikin masu laifin dayan kuma ya gudu 'Yan sanda sun kama wasu matasa guda biyu masu shekaru 17 da 14 da laifin yiwa wata mata fyade a kasar Afrika ta Kudu. 

  Matasan guda biyu sun yiwa matar mai shekaru 25 fyade wacce take 'yar madigo ce a cikin wani wuri a karshen makon da ya gabata. A rahoton da Daily Voice ta bayar mutane uku ne ake zargi da yiwa matar wannan aika-aika domin su gyara ta ta fara son maza. 


  Matasan sun yiwa budurwar fyade kwana daya kafin a gabatar da wani gagarumin biki a birnin Cape Town a ranar Asabar dinnan da ta gaba, wanda ake yin shi akan 'yancin masu auren jinsi, da kuma wayar da kan mutane kan auren jinsi.

  Da yake bayani akan lamarin, kwamandan ofishin 'yan sandan na Grassy Park, Colonel Dawood Laing, wanda yayi bayani a ranar Juma'a, matar tana kan hanyarta ta zuwa wani shago, a lokacin ne matasan suka kai mata hari. Laing ya ce daya daga cikin matasan ya sanya hannunshi a wuyan matar ya gaya mata cewa yana so yayi amfani da ita ne. 


  Sun yi mata kaca-kaca, sai ta gudu gida, amma 'yan gidansu duk sun yi bacci dole yasa ta hakura sai da safiyar ranar Asabar suka kai karar abinda ya faru ga 'yan sanda. A cewar Laing, mutanen yankin da 'yan sanda sun shiga tashin hankali dalilin wannan abu, kuma ya bayyana cewa za su yi iya bakin kokarinsu wajen gano mutum na uku da yake da hannu a lamarin. 


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI   • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Matasa sun yiwa budurwa 'yar madigo fyade domin su gyarata ta fara son maza Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI