MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"

Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Wednesday, March 4, 2020

  'Yan darikar 'Faidha' da ake zargi da yin wakar batanci ga Annabi sun tsallake rijiya da baya
  Mutanen wani gida da ke unguwar Sharifai a cikin birnin Kano sun sha da kyar bayan wasu fusatattun matasa sun kai farmaki unguwar tare da yunkurin kone musu gida bisa zarginsu da yin wata wakar batanci ga Annabi Muhammad (SAW). 


  A cewar jaridar Daily Trust, wani bincike ya gano cewa wani dan gidan mai suna, Yahaya Sharif Aminu, shine ya rera wakar da a cikinta aka yi amfani da kalaman batanci a kan manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi). Wakar, wacce nan da nan ta zagaya gari bayan an wallafa ta a dandalin sada zumunta, 


  ta fusata matasan da suka yi yunkurin kone gidan su mawakin kurmus. An gano cewa matashin mawakin, Yahaya Sharif Aminu, mabiyin mazhabar 'Faidha' ne a cikin darikar Tijjaniyya. 'Yan 'Faidha' sun yi kaurin suna wajen fifita soyayyar Shaikh Ibrahim Nyass a kan soyayyar annabi Muhammad (SAW) da Allah.

  Albarkar mata da kananan yara da ke cikin gidan yasa matasan basu cinna masa wuta ba, kamar yadda wata majiya ta sanar da Daily Trust.


   Fusattun matasa suna rushe gidan su matashi Yahaya Source: Facebook

  Wani shaidar gani da ido, Rabi'u Muhammad, ya bayyana cewa an kwashe mutanen gidan tare da boye su a wani gidan daban. Wasu mazauna unguwar Sharifai sun bayyana matukar kaduwa da mamaki a kan wakar da matashin ya wallafa.


  Malam Murabba'i, wani makwabci ga Yahaya, ya shaida wa manema labarai cewa basu yi tsammanin matashin zai aikata haka ba, saboda bashi da yawan hayaniya. Ya bayyana shi da mai shiru - shiru da babu alamun zafin akida a tare da shi duk da kowa ya san cewa dan darikar Tijjaniyya. Wannan ba shine karo na farko da mabiya 'Faidha' suka fara wallafar wakar da ta kawo hargitsi a Kano ba. Ko a cikin shekarar 2015 sai da gwamntin jihar Kano ta gurfanar da wani matashi, Abdul Nyas, a gaban kuliya bayan ya wallafa wata wakar batanci da rashin girmama Allah. LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI   • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: 'Yan darikar 'Faidha' da ake zargi da yin wakar batanci ga Annabi sun tsallake rijiya da baya Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI