\ Jami’ar Abubakar Olusola Saraki ta koma Jami’ar Kwara - Majalisar dokoki - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Jami’ar Abubakar Olusola Saraki ta koma Jami’ar Kwara - Majalisar dokoki - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: bzglobalservicelabari@gmail.com "Colour" <#20124d>
 • LABARAN YAU

  Wednesday, March 4, 2020

  Jami’ar Abubakar Olusola Saraki ta koma Jami’ar Kwara - Majalisar dokoki
  Da alamu rigimar Bukola Saraki da kuma gwamnatin jihar Kwara ta canza salo bayan da aka fara shirin sauyawa jami’ar gwamnatin jihar suna a makon nan. Kamar yadda mu ka samu labari ‘yan majalisar dokokin Kwara sun canzawa jami’ar Abubakar Olusola Saraki ta Kwara suna a Ranar Talatar nan da ta wuce. 


  ‘Yan majalisar dokokin jihar sun yi wa dokar da ta kafa jami’a jihar garambawul domin shafe sunan tsohon gwamnan daga cikin sunan jami’ar gwamnatin jihar. Wannan ya na cikin dokoki hudu da majalisar Kwara ta yi wa kwaskwarima a zaman da ta yi a farkon makon nan. Yanzu ana jiran gwamna ya sa hannu a kudirin. Da zarar gwamna ya rattaba hannu, sunan ya shiga doka. A cewar majalisar, kudirorin za su taimakawa ilmi kuma sha’anin shugabancin kananan hukumomi. 

  Majalisar jihar ta fitar da gajeren jawabi bayan ta yi wannan aiki, ta ce:


  Majalisar jihar Kwara ta na so a canzawa KWASU suna Source: Facebook 

  “Kudirin jami’ar Jihar Kwara na 2020, da ya canza sunan jami’ar daga jami’ar Abubakar Sola Saraki zuwa jami’ar jihar Kwara ya samu karbuwa a gaban majalisa.” ‘Yan majalisar su ka kara da cewa: “An mikawa Mai girma gwamna wannan kudiri domin ya sa hannu.” 


  Da zarar gwamna ya sa hannu, jami’ar za ta canza suna. Dr. Bukola Saraki ne ya gina wannan jami’a a Garin Malete a 2009 lokacin ya na gwamna. Saraki ya yi mulki a Kwara daga 2003 zuwa 2011 a karkashin jam’iyyar PDP. Bayan ya sauka daga kujerar gwamna, Saraki ya tafi majalisar dattawa. Saraki wanda ya bar PDP a 2014 ya sake dawowa jam’iyyar a 2018, amma ya fadi zaben 2019. Ana zargin cewa rigimar tsohon shugaban majalisar da sabon gwamnatin jihar Kwara ta APC ta na cikin abin da ya sa majalisa su ka fara shirin canzawa jami’ar suna. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI   • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Jami’ar Abubakar Olusola Saraki ta koma Jami’ar Kwara - Majalisar dokoki Rating: 5 Reviewed By: Admin