MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"
 • Latest News

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Wednesday, March 4, 2020

  Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da Oshiomhole daga matsayin Shugaban APC

  - Wata babbar kotun birnin tarayya a Jabi, Abuja ta dakatar da Adams Oshiomhole daga matsayin Shugaban jam’iyyar APC na kasa - Alkalin kotun, Justis Danlami Senchi, a ranar Laraba, 4 ga watan Maris, ya umurci Oshiomhole da ya sauka zuwa lokacin da za a yanke hukunci - An dai shigar da wata kara ne inda aka bukaci kotu da ta tsige Oshiomhole daga matsayin shugaban APC:

  Wata babbar kotun birnin tarayya a Jabi, Abuja ta dakatar da Adams Oshiomhole daga matsayin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa. Justis Danlami Senchi, a ranar Laraba, 4 ga watan Maris, ya umurci Oshiomhole da ya sauka zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar da ce neman a tsige shi daga matsayin Shugaban APC na kasa. Zuwa yanzu dai babu cikakken labari kan rahoton.

  Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da Oshiomhole daga matsayin Shugaban APC Source: Depositphotos 


  A baya mun ji cewa shugaban jam’iyyar APC mai mulki Adams Oshiomhole ya na fuskantar kalubale bayan gwamnonin jam’iyyar sun shiga cikin masu taso sa. Jaridar tace idan aka tafi a haka, kwanakin Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyya na kasa su na daf da zuwa karshe har an fara tunanin zai iya rasa mukaminsa a farkon shekarar 2020. 

  Hakan na zuwa ne bayan da aka fara jin kishin-kishin cewa wasu daga cikin gwamnonin APC sun bi zugar da ke neman ganin bayan shugaban jam’iyyar. Yanzu dai Oshiomhole ya na kan siradi. 

  Majiyar Jaridar ta Daily Sun tace abin da ya ke ceton Oshiomhole a wannan lokaci kurum shi ne sa bakin da fadar shugaban kasa ta yi a cikin rikicin. A wani bangare, an musanya wannan jita-jita. Rahotanni sun ce gwamnonin za su nemi a tsige Oshiomhole muddin ya ki bin hanyar lalama ya ajiye aikin da kansa. Sai dai Hadimin shugaban jam’yyar, Simon Ebegbulem ya karyata wannan.LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI   • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da Oshiomhole daga matsayin Shugaban APC Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI