\ Magidanci ya kashe kansa da kansa bayan ya gano matarsa tana neman maza - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Magidanci ya kashe kansa da kansa bayan ya gano matarsa tana neman maza - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: bzglobalservicelabari@gmail.com "Colour" <#20124d>
 • LABARAN YAU

  Wednesday, March 4, 2020

  Magidanci ya kashe kansa da kansa bayan ya gano matarsa tana neman maza

  Wani magidanci dan shekara 48 mai suna Felix Edore ya halaka kansa ta hanyar kwankwadar kwalar fiya fiya biyo kama matarsa da ya yi da laifin cin amanarsa ta hanyar neman maza duk kuwa da cewa igiyar aurensu na daure. Jaridar Punch ta ruwaito Felix ya yanke ma kansa wannan danyen hukunci ne sakamakon bacin rai da ya shiga a sanadiyyar bankado asirin matarsa wanda suka kwashe shekaru 16 suna tare, ashe a bayan idon sa tana neman maza. 

  Majiyarmu ta ruwaito Felix yana sana’ar tuka motar Tasi ne daga Abraka-Etsu zuwa Sapele a jahar Delta, ya kwankwadi fiya fiya ne a ranar Juma’ar da ta gabata a garin Sapele, inda aka garzaya da shi zuwa asibiti, a washegarin Asabari ya mutu, kamar yadda likitoci suka tabbatar. Makwabtansu sun bayyana Felix a matsayin mutumin kirki wanda yake jin dadin sana’ar da yake yi, kuma bai dade da sayen motar da yake amfani da ita ba. 

  Ita ma wata makwabciyarsu mai suna Mama Rita ta bayyana cewa: “Felix ya kashe kansa ne bayan ya tabbatar da zargin da yake ma matarsa na neman maza, yaransu 6, kuma ya dade yana korafi kan halinta na neman maza, sau da yawa sun sha rikici a kan maganan, 

  inda aka saba jiyo shi yana barazanar kashe kansa saboda ita. “A wannan rana bamu san ya sayo fiya fiya ba, ko kafin mu ankara har ya kwankwadi abinsa tun a cikin mota, daga nan ne jama’a suka hange shi, suka mika shi zuwa asibiti, inda a can ya mutu.” Inji ta. 

  A wani labarin kuma, kwana dubu na barawo, kwana daya rak na mai kaya kamar yadda kwamishinan Yansandan jahar Delta, Hafiz Inuwa ya sanar da kama wasu miyagun mutane masu sata tare da garkuwa da jama’an da basu ji ba, basu gani ba. 

  Kwamishina Inuwa ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Warri inda yace Yansanda sun kama barayin ne a tsakanin ranakun Lahadi da Litinin a Oghara, karamar hukumar Ethiope ta yamma. A cewar kwamishinan, mutane hudu daga cikinsu sun amsa laifin satar wata mata mai suna Victoria Okereka daga asibitinta a ranar 22 ga watan Feburairu, wanda suka saketa bayan ta kwashe kwana guda a hannunsu. 


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI   • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Magidanci ya kashe kansa da kansa bayan ya gano matarsa tana neman maza Rating: 5 Reviewed By: Admin