--
Hotunan bindigu, alburusai, kudi da kwayoyi da rundunar 'yan sanda ta kama tare da masu garkuwa da mutane a Abuja

Hotunan bindigu, alburusai, kudi da kwayoyi da rundunar 'yan sanda ta kama tare da masu garkuwa da mutane a Abuja

A ranar Laraba ne rundunar 'yan sanda a Abuja ta yi bajakolin masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami da jami'an tawagar yaki da fashi da makami (SARS) suka kama a jihohi daban - daban. 

Daga cikin miyagun kayayyakin da aka samu a wurin masu laifin akwai bindigu 30 da suk hada da AK47 da kuma wasu na gida, carbi 1520 na alburusai, miyagun kwayoyi da kuma makudan takardun kudi. Yayin bajakolin masu laifin, wasu daga cikinsu sun nuna yadda suke boye bindigu a jikin babur da mota yayin da za su fita ofireshon.

Da yake magana yayin bajakolin masu laifin, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, DCP Frank Mba, ya ce rundunar 'yan sanda ba zata sassauta ba wajen yaki da rashin tsaro a cikin kasa.

Hotunan masu laifi da miyagun kayayyakin da aka samu tare da su: 





LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Hotunan bindigu, alburusai, kudi da kwayoyi da rundunar 'yan sanda ta kama tare da masu garkuwa da mutane a Abuja "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?