--
Sarkin Loko ya fadi abinda suka tattauna da Sanusi a daren da ya kwana a garinsa

Sarkin Loko ya fadi abinda suka tattauna da Sanusi a daren da ya kwana a garinsa

Alhaji Abubakar Ahmed Sabo, sarkin garin Loko, a jihar Nasarawa, inda aka fara bawa Alhaji Muhammadu Sanusi II masauki da farko kafin a mayar da shi Awe ya bayyana abubuwan da suka tattauna da tubaben sarkin.

Basaraken na Loko ya ce ko kadan Sanusi bai damu da cire shi daga kan mulki da aka yi ba kuma ya kira sabon sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya taya shi murna bisa sarautar da ya samu kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A hirar da ya yi da BBC Hausa a ranar Laraba, ya bayyana cewa Sanusi ba zai kallubalanci cire shi da aka yi daga mulki ba a kotu inda ya shawarci masu rike da sarautun gargajiya su yi takatsantsan wurin harka da 'yan siyasa.

Ya ce, "Hankalin Sanusi kwance a lokacin da ya iso nan, ya yi barcinsa lami lafiya kuma ya rungumi abinda ya faru da shi a matsayin kaddara. Ya kuma ce bai zai tafi kotu domin kallubalantar cire shi ba. Ya fadawa al'umma su bawa sabon sarki Aminu Ado Bayero goyon baya. Ya ma aike wa Alhaji Aminu Ado Bayero sakon taya murna.

"Sanusi ya shawarci masu rike da sarautun gargajiya su yi takatsantsan wurin harka da 'yan siyasa domin ba komai ne ya janyo aka cire shi ba illa siyasa.

"Sarki Sanusi ya ce bai yi nadamar wani abu da ya aikata ba domin bai aikata laifi ba."

Da ya bayar da dalilan da yasa aka dauke Sanusi daga Loko zuwa Awe bayan kwana guda daya a kauyen, Sabo ya ce garin ya yi wa tsohon sarkin kauye domin babu isasun abubuwan more rayuwa.

Ya ce, "Sarki Sanusi ya fi karfin wannan wurin. Babban mutum ne shi kuma kamata ya yi ya zauna a wurin da akwai na'urar sanyaya daki (AC) amma ba mu da wutan lantarki da zamu samar masa wannan."


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Sarkin Loko ya fadi abinda suka tattauna da Sanusi a daren da ya kwana a garinsa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?