Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com "Colour"
 • LABARAN YAU

  Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki,

  ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________
  Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views

  Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Tuesday, March 3, 2020

  EFCC ta cafke wata mata da ta damfari Hadiza Inna Sanusi N36m a Kano

  A ranar Talata ne hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta gurfanar da wata mata mai suna Asiya Bala Aliyu, a gaban wata babbar kotu da ke jihar Kano, bisa tuhuma guda biyu da suka hada da damfara da karkatar da kudade. A cikin jawabin da shugaban sashen yada labarai da sanarwa a hukumar EFCC, Tony Orilade, ya fitar, 

  ya bayyana cewa Asiya ta karbi kudi, miliyan N36, daga hannun Hadiza Inna Sanusi da sunan saka hannun jari a wani tsarin kasuwanci mai suna 'Galaxy Investment Package'. Sai dai, Asiya ta karkatar da kudin da ta karba tare da yin amfani da su wajen kashe matsalolin kanta. Daya daga cikin tuhumar na cewa: "ke, Asiya Bala Aliyu,

   a wani lokaci da ya wuce, tsakanin watan Mayu da Agusta na shekarar 2018, kin karbi kudi miliyan talatin da biyar (N35,000,000) daga hannun Hadiza Inna Sanusi, da sunan saka jari a wata harkar kasuwanci, amma kika nuna rashin gaskiya tare da lalata kudin da kika karba. Yin hakan ya saba da sashe na 308 kuma an tanadi hukucinsa a karkashin sashe na 309 na kundin dokoki da hukuncin laifuka." 

  Asiya Aliyu da jami'ar EFCC Source: Twitter Lauyan hukumar EFCC, Musa Isah, ya roki kotun ta saka ranar fara shari'a da Asiya domin tabbatar wa da alkali cewa tana da laifi. Khalid Kashim Njidda, lauyan da ke kare wacce ake kara, ya mika bukatar neman kotu ta bayar da belin wacce ya ke kare wa.

  Sai dai, lauyan EFCC ya soki bukatar neman bayar da belin Asiya. Kazalika, ya soki bukatar neman a tsare ta a ofishin EFCC har zuwa lokacin zaman kotun na gaba, kamar yadda lauya Njidda, da ke kare Asiya, ya nema. Alkalin kotun, Jastis R. A Sadiq, ya amince da bukatar lauyan hukumar EFCC tare da saka ranar 12, ga watan Maris, 2020 domin sauraron bukatar neman baya da belin Asiya tare da fara shari'ar tuhumar da ake yi mata 


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 


  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: EFCC ta cafke wata mata da ta damfari Hadiza Inna Sanusi N36m a Kano Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI