Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Tuesday, March 3, 2020

  Auren mace fiye da daya ya fi bibiyar matan banza - Binta ta shawarci maza

  - Zancen auren mace fiye da daya har yanzu yana jawo cece-kuce daga bangarori da dama na Najeriya - Amma kuma abu daya ne wanda kowa ya san shi, shine mata sun fi maza yawa - Binta tayi kira ga maza a kan su ji tsoron Allah kuma su auri mace fiye da daya Zancen auren mace fiye da daya har yanzu yana jawo cece-kuce daga bangarori da dama na Najeriya.

   Daga tsokacin da ake samu kuwa, mata na ci gaba da sukar auren mace fiye da daya. Wasu mata ko maza da suke sukar auren mace fiye da dayan na kafa hujjoji ne daga mahangar addinin Kirista. Amma kuma abu daya ne wanda kowa ya san shi, shine mata sun fi maza yawa. Idan kuwa aka dubi hakan,

  wa zai auri matan da basu riga sun yi aure ba? Wani abu da ake mantawa kuwa shine, ba kowanne namiji bane yake iya zama da mace daya ba. Hakazalika, namiji mai shekaru 100 zai iya yi wa mace ciki amma matan masu shekaru da yawa basu iya dauka. 

  Auren mace fiye da daya ya fi bibiyar matan banza - Binta ta shawarci maza Source: Getty Images 

  Wannan lamarin kuwa yasa maza suke fadawa neman matan banza koda kuwa suna da aure. A yayin da yawaitar zawarawa da kuma neman mata yake ci gaba, wata mata ta shawarci mata a kan mazansu masu yunkurin auren mata su kawo gidansu. Ta bukaci matan da su saka ransu a cikin salama tare da yarjewa mazansu auren wasu matan.


  Ta ce: "Yan uwana maza, ku auri mata a maimakon ku dinga neman mata bayan kuna da aure." Tayi kira ga maza a kan su ji tsoron Allah kuma su auri mace fiye da daya. Ta kammala da cewa "ku ji tsoron Ubangiji ku auri mata." 


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 


  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Auren mace fiye da daya ya fi bibiyar matan banza - Binta ta shawarci maza Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI