\ Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: bzglobalservicelabari@gmail.com "Colour" <#20124d>
 • LABARAN YAU

  Tuesday, March 3, 2020

  Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya


  Kashe-kashen musulmai a kasar Indiya sakamakon hargitsi tsakanin Musulmai da mabiya addinin Hindu a kan wata doka ya zamo sanadin rasa rayuka 27 a birnin New Delhi a ranar Laraba. A yayin da babban birnin kasar Indiyan ke fuskantar hari mafi muni a kan Musulmai a wannan lokacin, Firam minista Narendra Modi ya wallafa 

  "Ina kira ga 'yan uwana maza da mata da ke Delhi a kan su zauna lafiya cikin kaunar juna a kowanne lokaci" a shafin shi na tuwaita. 'Yan sanda da sauran jami'an tsaron farin kaya na ta sintiri a titunan a ranar Laraba. Wasu yankunan da aka yi zanga-zanga a su duk an tarwatse. Modi yayi kiran ne bayan caccakar shi da 'yan jam'iyyun adawa suka yi a kan gazawar gwamnatin shi a wajen dakatar da wannan rikici duk da amfani da barkonon tsohuwa, 

  duwatsu da kuma hayaki da masu zanga-zangar ke yi. Shugaban jam'iyyar adawa, Sonia Gandhi yayi kira ga ministan lamurran cikin gida, Amit Shah a kan yayi murabus, wanda alhakin aiwatar da doka a babban birnin ya rataya a kan shi. A wani bangare kuwa, Ajit Doval, mai bada shawara a kan tsaron kasar, 

  wanda alhakin kwantar da tarzomar birnin Delhi din ta rataya a kan shi, ya kara ziyartar Jafrabad a yammacin Laraba don duba yanayin tsaron da kuma yin jawabi ga jama'ar. "Da izinin Allah zaman lafiya zai wanzu," ya ce a yayin da yake kewaye da tawagar jami'an tsaro. "An shawo kan komai kuma jama'a sun gamsu. Ina da tabbacin cewa hukumomin tsaro na yin abinda ya dace." Ya kara da cewa.

  Jafrabad na daya daga cikin yankin da tarzomar ta fi tashi a birnin New Delhi. Kwanaki hudu kenan da ake ta tashin hankulan inda aka kashe mutane 27 tare da raunata mutane 200. A wannan yankin ne kuma aka samu wata budurwa da ta tsare Doval inda ta sanar da shi cewa ita daliba ce kuma basu iya bacci da dare. Rikicin bai ritsa da ita ba amma kuma bata iya karatu. 

  "Kada ki damu. Wannan alhakin gwamnati ne da jami'an tsaro. Nayi alkawari," NSA ya sanar da ita. Doval ya ziyarci babban birnin kasar India din wajen da matsalar ta auku sannan ya gana da jami'an tsaro har da babban ministan Arvind Kejriwal amma tarzomar bata lafa ba. Ya kara da ziyartar Seelampur, Maujpur da kuma Gokulpuri Chowk. "Mutane na tantamar jami'an 'yan sandan Delhi din amma akwai bukatar a amince da masu khaki," ya ce a lokacin da tarzomar ta sake ballewa. LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 


  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya Rating: 5 Reviewed By: Admin