Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Friday, March 20, 2020

  Budurwa dauke da tsohon ciki ta sha guba bayan ta gano cewa saurayinta yana da aure

  A ranar Alhamis dinnan ne wata budurwa mai shekaru 20 daga jihar Anambra tayi kokarin kashe kanta bayan ta gano cewa saurayinta yana da aure Budurwar ana zargin ta sha guba ne domin ta kashe kanta kowa ma ya huta. 

  Budurwar da aka bayyana sunanta da Oluchi daga garin Obosi dake cikin karamar hukumar Idemili cikin jihar ta Anambra. Rahotanni sun bayyana cewa an ceto rayuwarta sannan kuma 'yan sanda suka kama ta da zargin kokarin kashe kanta. Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin. 

  Ya ce: "A ranar 19 ga watan 3 shekarar 2020 da misalin karfe 4 na yamma, an kai rahoto ofishin 'yan sanda na Awada cewa wata budurwa mai karancin shekaru da aka bayyana sunanta da Oluchi Akabilo ta sha guba da niyyar kashe kanta.

  "Budurwar ana zargin tana da ciki da saurayin nata mai suna Chinedu wanda ba a san ainahin sunan mahaifinsa ba, an bayyana cewa yana da aure har da 'ya'ya. "Hankalinta yayi matukar tashi bayan ta gano cewa yana da aure, inda taje ta sayo guba da kudin da saurayin ya bata naira dubu goma domin ta zubar da cikin da ta dauka. "An garzaya da ita asibiti mafi kusa dake garin Onitsha, 

  inda 'yan sanda suka kai ta kuma likitoci suka yi iya bakin kokarinsu domin su ceto rayuwarta. Jami'in hulda da jama'a na hukumar ya kara da cewa: "Yanzu haka muna cigaba da gabatar da bincike akan lamarin, kuma mun sanya jami'anmu su nemo duk inda saurayin ya shiga, domin tabbatar da ainahin abinda ya faru." 


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Budurwa dauke da tsohon ciki ta sha guba bayan ta gano cewa saurayinta yana da aure Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI