MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"
 • Latest News

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Friday, March 20, 2020

  A gaban Uban da ya haifeni ma na sha shisha ballantana a gabanku - Martanin Tumba Gwaska ga masu zaginta  - Jaruma Tumba Gwaska ta mayarwa da mabiyanta da suka yi caa a kanta martani kan wani bidiyo da ta saki 


  - Jarumar dai ta saki bidiyon ne tana shan shisha, hakan ya sanya da yawa daga cikin mabiyanta suka fara zaginta 

  - Ta bayyana cewa a gaban mahaifin da ya haifeta ma tasha shisha ballantana kuma a gaban wasu Ga dukkan alamu mabiyan jaruma Tumba Gwaska sun kaita makurar bacin rai wanda har ta kai ga ta wallafa wani bidiyo tana musu martani kan cece-kucen da suke akan ta kan tayi bidiyo tana shan shisha. 


  Cikin fushi jarumar ta wallafa wani bidiyo, inda take martani ga masu zargin ta kan sun ganta da shisha, ta bayyana musu cewa tsarin rayuwar ta daban da tasu kuma ita 'yar Niger ce, 'yar Faransa, dan tana shan shisha zata yi bidiyo ba ta ga dalilin da zai sa ta ajiye shishar ba tunda ta sha a gaban mahaifinta ma balle wasu. 


  Jarumar ta kara da cewa ita ba 'yar kwaya bace shisha ce kawai take sha kuma ta nunawa duniya kuma duk wanda ya zage ta sai ta rama tunda uwa bata fi uwa ba, kuma tana daukar sunan masu zagin nata zasu san ko ita wacece zata dauki mataki.


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: A gaban Uban da ya haifeni ma na sha shisha ballantana a gabanku - Martanin Tumba Gwaska ga masu zaginta Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI