LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yadda takalma suka tona wa wasu 'yan fashi da makami asiri a Zaria


Wani shaida mai suna Sajan Jamilu Tanimu da ke aiki da ofishin ‘yan sanda a Zaria, ya labarta yadda takalman da aka bari a wajen da aka yi fashi da makami suka tona asrin ‘yan fashin. Tanimu yaa bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayin da yake bada shaida a gaban wata kotun majistare da ke Zaria, 

kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Dan sanda mai gabatar da karar, Sajan Yau Garba, ya fara gabatar da karar ne a ranar 20 ga watan Fabrairun 2020. Wadanda ake karar kuwa masu suna Isah Abdullahi da Mubarak Abdullahi dukkansu masu shekaru 17 ne 

daga anguwan Dan Madami a birnin Zaria. Mai gabatarwar ya ce wadanda ake karar ana zarginsu ne da hada kai wajen aikata laifi, balle gida da kuma tsoratarwa wanda hakan ya ci karo da sassa na 58, 327, 377, 270 da 332 na dokokin Penal Code na jihar Kaduna. Shaidar ya sanar da kotun cewa, a ranar 6 ga watan Fabrairu wajen karfe 10:30 na dare sun fasa gida, sun yi sata tare da tsorata wanda yayi kara mai suna Alhaji Yahaya Sani.

Tanimu ya ce mai karar ya bayyana yadda ‘yan fashi suka shiga mishi gida tare da kwashe musu kayayyaki amma sai suka bar takalmansu. Bayan kwanaki tara kuwa sai aka kama Isah na sata a wani gida da ke kusa da na wanda ya kai korafin. “A yayin bincike, 

Isah ya bayyana cewa tare suke da Mubarak. Amma kuma daga baya sai suka musanta zargin da ake musu,” yace. Bayan tsananta bincike ne aka gano cewa wadannan takalman mallakin Mubarak ne. Amma kuma har yanzu ba a kama komai ba daga cikin abinda aka sata a hannunsu. Hakazalika, shaidar ya kasa yin bayanin yadda takalman suka kai gidan mai korafin. Alkali Ruqayyat Ummi Ahmed ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Maris don ba wa mai gabatar karar kawo shaidarsa.  


LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
Post a comment

0 Comments