--
Bidiyon tsiraici: Maryam Booth ta shigar da karar tsohon saurayinta, ta nemi ya biyata N300m

Bidiyon tsiraici: Maryam Booth ta shigar da karar tsohon saurayinta, ta nemi ya biyata N300m


Sananniyar jarumar fina-fina Hausa, Maryam Booth, ta maka tsohon saurayinta, Ibrahim Ahmed Rufai a gaban kotu sakamakon zarginsa da ta ke da yada bidiyon tsiraicinta ba tare da izininta ba. Idan za mu tuna, makonni kadan da suka gaba ne kafafen sada zumuntar zamani suka hautsine da bidiyon tsiraicin jarumar. Lamarin da ya jawo martani da cece-kuce daga jama'a masu tarin yawa. Bayan kwanaki kadan da walllafa wannan bidiyon, 


jarumar ta fito ta bayyana wanda ta ke zargi da wannan aika-aikar. Ta ce tsohon saurayinta kuma matashin mawaki Deezell ne da wannan aika-aikar. A don haka ne kuwa jarumar ta sha alwashin daukar matakin shari'a a kan tsohon saurayin nata da ya ci amanarta. 

A karar da ta shiga a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020 a gaban wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayyar Abuja, Booth ta yi ikirarin cewa tsohon saurayin nata ya dauka wannan bidiyon ne ba tare da izininta ba a ranar 27 ga watan Fabrairun 2017 a dakin otal din Nanet Suit da ke Abuja.

A don haka ne kamar yadda ta ce, wanda take karar ya fara yi mata barazanar sakin bidiyon tsiraicin na ta tare da bukatar wasu kudi daga hannunta. Ya ce zai wallafa bidiyon matukar ba ta bashi kudin ba. 


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 


0 Response to "Bidiyon tsiraici: Maryam Booth ta shigar da karar tsohon saurayinta, ta nemi ya biyata N300m "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?