\ Fitattun 'yan siyasa 12 da suka mutu sakamakon hatsarin mota - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Fitattun 'yan siyasa 12 da suka mutu sakamakon hatsarin mota - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: bzglobalservicelabari@gmail.com "Colour" <#20124d>
 • LABARAN YAU

  Sunday, March 1, 2020

  Fitattun 'yan siyasa 12 da suka mutu sakamakon hatsarin mota

  A Najeriya dai mutane da dama na rasa rayukansu sakamakon hadurra a kan titunan kasar. Hadurra kuwa na faruwa ne saboda rashin kyan tituna da lalacewarsu. Sau da yawa dai jama'a na kokawa da yadda wasu titunan kasar nan suka lalace. Ga wasu sanannun 'yan siyasa da suka rasa rayukansu sakamakon hadurra a kan titunan Najeriya. 

  1. Adegoke Adelabu Yana daya daga cikin ‘yan siyasar farko na Najeriya da ya rasu sakamakon hatsarin mota. Shine shugaban NCNC kuma tsohon dan siyasa a yankin yammacin kasar nan. Abokin adawar Chief Obafemi Awowolo ne wanda ya kirkiro Action Group. 

  2. Dr. Joe Ukpo Dan kasa ne nagari kuma ma’aikacin gwamnati. Ya rasu ne sakamakon mummunan hatsarin motar da ya faru a ranar 15 ga watan Afirilun 2018. An gano cewa yana kan hanyarsa ta zuwa Okpoma/Okuku a jihar Cross River daga Abuja. Ya mutu bayan sa’o’i kadan da aukuwar hatsarin. 

  3. Dr. Matthew Achigbe Shine shugaban jam’iyyar APC na jihar Cross River. Ya rasa ransa ne sakamakon hatsarin motar da ya faru a ranar 16 ga watan Nuwamban 2018 a kan titin Afikpo da ke jihar Ebonyi. Yana kan hanyar zuwa coci ne da ke jihar Enugu.

   4. Chief James Ocholi (SAN) Ya yi karamin ministan kwadago. Ya rasu ne tare da matarsa da kuna dansa a mummunan hatsarin da ya faru a ranar 16 ga watan Maris 2016. Hatsarin ya auku ne a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. 

  5. Sakiru Alabi Balogun Sakiru dan takarar shugabancin karamar hukumar Ikotun/Igando ne a karkashin jam’iyyar APC. Ya rasu ne a hatsarin ranar 21 ga watan Yulin 2017 a kan titin LASU/Isheri da ke yankin Igando. An gano cewa komai na kamfen dinsa na tafiya dai-dai a lokacin da ya rasa rayuwarsa. 

  6. Genera John Shagaya Shi ne tsohon ministan al’amuran cikin gida. Ya rasu ne a hatsarin motar da ya faru na ranar 11 ga watan Fabrairun 2018. Ya rasu yana da shekaru 75 a duniya.

  7. Alhaji Auwal Jallah Alhaji Auwal Jallah ne mai magana da yawun jam’iyyar APC ta jihar Bauchi. Ya rasu ne a hatsarin da ya auku na ranar 4 ga watan Disamban 2017. Lamarin ya auku ne a kan babban titin Azare zuwa Gamawa na jihar Kano. 
  span style="font-family: "open sans" , "arial" , sans-serif; font-size: 18px;">
  8. Sanata Usman Bashir Tsohon dan majalisar dattijan ne daga jihar Yobe. Ya rasu ne a hatsarin da aka tafka na ranar 2 ga watan Yulin 2012 a kan titin kano zuwa Zaria.


   9. Olufunsho Martins (AVM) Ya rasu ne a ranar 28 ga watan Oktoban 2017. Ya yi hatsarin ne a kusa da jami’ar jihar Legas. Hatsarin ya kai ga har motarsa ta fada cikin ruwan kogin Legas amma daga baya an samo gawarsa a ciki. 


  10. Hajiya Aisha Tahir Ita ce shugaban mata ta jam’iyyar APC a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa. Ta rasu ne tare da wasu mutane shida na jam’iyyar a ranar 23 ga watan Janairun 2019. Sun dawo daga gangamin kamfen ne a jihar. 

  11. Sanata Mukhtar Abdulkarim Dan asalin jihar Zamfara ne daga karamar hukumar Talatan Mafara amma an haifesa a garin Zurmi ne. Ma’aikacin gwamnati ne, dan siyasa, malami kuma mai habaka al’adu. Ya rasu ne tare da dan uwansa da kuma direbansa a hatsarin ranar 23 ga watan Disamba. Babbar mota ce ta nikesu a kan titi. 


  12. Abdulkareem Adisa Shine tsohon gwamnan jihar Oyo a zamanin mulkin soja. Ya rasu ne a wani asibitin da ke London sakamakon hatsarin mota da yayi. Dan asalin jihar Kwara ne kuma yana cikin wadanda ake zargi da sa hannu a mutuwar marigayi Sani Abacha. 

  ALLAH YAJIQAN MUSULMI AMEEN 

  DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI DA SAURAN RUBUTUTTUKA TA WHATSAPP LATSA NAN👉👉https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

  KUBIYOMU A FACEBOOK FAGE KUYI LIKE  
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Fitattun 'yan siyasa 12 da suka mutu sakamakon hatsarin mota Rating: 5 Reviewed By: Admin