\ A karon farko: Shugaba Buhari ya yi magana a kan bullar 'Coronavirus' a Najeriya - BZGLOBALSERVICE.COM.NG A karon farko: Shugaba Buhari ya yi magana a kan bullar 'Coronavirus' a Najeriya - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: bzglobalservicelabari@gmail.com "Colour" <#20124d>
 • LABARAN YAU

  Monday, March 2, 2020

  A karon farko: Shugaba Buhari ya yi magana a kan bullar 'Coronavirus' a Najeriya

  Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi kira ga 'yan Najeriya a kan kada su tsorata kan barkewar cutar Coronavirus. Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Najeriya ta bayyana samun mai cutar a makon da ya gabata. Wani dan kasar Italiya ne ya iso Najeriya da cutar kuma aka killace shi.


  Cutar ta jawo halakar kusan mutane 3,000 a duniya, inda mafi yawa an mutu ne a kasar China inda cutar ta fara. A wata takardar da mai magana da yawun fadar shugaban kasar, Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari yayi kira ga 'yan Najeriya "a kan kada su tsorata da sabuwar cutar Covid-19 din da ta shigo kasar nan."  Ga cikakkiyar takardar: Da tsananin alhini Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jajanta shigowar cutar Covid-19 a jihar Legas da ke Najeriya. Akwai kokari da jajircewar gwamnatocin jihohi wajen kafa cibiyoyin gaggawa da kuma hanyoyin kare yaduwar cutar.


  A don haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa kokarin ma'aikatar lafiya ta tarayya da sauran cibiyoyi a kan jajircewarsu da kwarewarsu wajen bankado cutar. Sun dau matakin gaggaawa wajen gano wadanda mai cutar yayi mu'amala da su. 


  Shugaban kasar ya jinjinawa ma'aikatar lafiya ta tarayya da kuma gwamnatin jihohin Legas da Ogun da suka kai rahoton lamarin kuma suka jawo hankulan jama'a tare da wayar musu da kai. Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga 'yan Najeriya da su saurari shawarwarin ma'aikatar lafiya da cibiyar kiwon lafiya ta duniya. An watsa wannan ne a duk kafafen yada labarai daga ma'aikatar yada labaran Najeriya 

  Garba Shehu Babban mai bada shawara ga shugaban kasa a kan yada labarai. 


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 


  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: A karon farko: Shugaba Buhari ya yi magana a kan bullar 'Coronavirus' a Najeriya Rating: 5 Reviewed By: Admin