--
Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa na Jam'iyyar ANPP Ya Bayar da Tallafin N50,000,000 ga........

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa na Jam'iyyar ANPP Ya Bayar da Tallafin N50,000,000 ga........

 JARI/TALLAFIN NAIRA MILLIYAN HAMSIN (#50,000,000) GA AL'UMAR KIRU/BEBEJI DAGA HON ABDULMUMIN JIBRIN KOFA PhD.


A jiya 31/12/2022, dan takarar majalissar tarayya a kananan hukumomin Kiru/Bebeji a jam'iyyar NNPP Hon Abdulmumin Jibrin Kofa PhD,(Jarman Bebeji) ya gwanjage mutanen yankinsa da jari/tallafin kudade inda wasu suka rabauta da Dubu dari biyu(#200,000), Dubu dari daya(#100,000), Dubu Hamsin(#50,000), Dubu Ashirin(#20,000), Dubu Goma(#10,000) da kuma Dubu Biyar(#5,000).


Mutanen da suka amfana da wannan jari/tallafi sun hada da wakilan akwatuna, Exco na karamar hukuma da mazabu na Jam'iyyar NNPP da PDP na Kiru/Bebeji, KOKAS na Kiru/Bebeji, Wasu kungiyoyi masu karfi na mata da matasa a Kiru/Bebeji, Dagatan Kiru/Bebeji, Limaman Juma'a Kiru/Bebeji, Malaman Kwankwasiyya Kiru/Bebeji, Dalibai, Yan Social Media, Mafarauta, Yan Achaba, Mahauta da kuma mutane masu bukata ta musamman.


Wannan taro ya sami halartar yan takarkaru na Kiru/Bebeji, manyan jagorori tare da  shuwagabannin jam'iyyar NNPP/PDP na Kiru/Bebeji.

















0 Response to "Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa na Jam'iyyar ANPP Ya Bayar da Tallafin N50,000,000 ga........"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?