--
"Ya zo har gidana ya yi min jajen batarta, yana kuka" Mahaifin Hanifa Abubakar, Malam Abubakar Abdulsalam Acikin wannan Bidiyon

"Ya zo har gidana ya yi min jajen batarta, yana kuka" Mahaifin Hanifa Abubakar, Malam Abubakar Abdulsalam Acikin wannan Bidiyon


Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ranar Laraba ne dai dubun Tanko ta cika, bayan da ya ɗauke Hanifah tsawon sama da kwanaki 40, inda da ga bisani ya kashe ta bayan ya karɓi wani abu daga cikin naira miliyan 6 da ya ce a bashi kuɗin fansa.


KUNA IYA KALLON BIDIYON HIRAR DA AKAYI DA MAIHAIFIN HANIFA KU LATSA HOTON DAKE KASA DOMIN KALLON BIDIYON: 


Yadda mahaifiyar Hanifah ta nannaushi malamin da yai garkuwa da kashe ƴar ta a Kano

Mahaifiyar Hanifah Abubakar, ƴar shekara 5 da malamin makarantar su Noble Kids Academy, Abdulmalik Tanko, ta fusata ta nannaushe shi bayan da ƴan sanda su ka kawo shi Shalkwatar Ƴan Sanda a Kano.




A yau Juma'a ne Rundunar Ƴan Sanda ta yi holon Tanko da sauran waɗanda ake zargi da hannu a kashe yarinyar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa su ma iyayen marigayiya Hanifah sun zo shelkwatar ƴan sandan.

Jaridar ta ce iyayen Hanifah ne su ka fara zuwa wajenz inda da ga bisani sai a ka kawo Tanko da sauran waɗanda a ke zargi.

Da ga zuwan masu laifin, sai mahaifiyar Hanifah, Fatima Maina, ta hango Tanko, in da ta yi kansa, ta cakumo shi, sannan ta riƙa zabga masa mari da naushi.

Lamarin ya sanya ƴan sanda su ka zaburar su ka ɗauke Tanko ɗin, inda saura kuma su ka riƙa baiwa Fatima haƙuri.

0 Response to ""Ya zo har gidana ya yi min jajen batarta, yana kuka" Mahaifin Hanifa Abubakar, Malam Abubakar Abdulsalam Acikin wannan Bidiyon"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?