--
Daga zanga-zanga, mutane masu nakasa sun nakadawa jami'in tsaro duka a kofar majalisa (Bidiyo)

Daga zanga-zanga, mutane masu nakasa sun nakadawa jami'in tsaro duka a kofar majalisa (Bidiyo)

Nakasassu sun fusata ranar Alhamis a majalisar dokokin tarayya dake Abuja - An samu sabani tsakaninsu da jami'an dake gadi kofar shiga majalisa Wasu mutane masu nakasa sun garzaya majalisar dokokin tarayya domin zanga-zanga a ranar Alhamis, 17 ga watan Disamba, 2020. 



Amma yayin zanga-zangar, wani jami'in tsaro ya gamu da fushinsu inda suka lakada masa mumunan duka. The Nation ta ruwaito cewa mambobin kungiyar nakasassun yankin Neja Delta, Great-Mind Foundation, sun dira majalisar ne domin ganin sanatocin da ke wakiltansu a majalisar dattawan tarayya.


Sun lashi takobin cewa ba zasu bar majalisa ba har sai sun gana da Sanatocin domin gabatar da bukatunsu. Daga cikin abubuwan da suke so shine a koya musu ayyukan hannu da kuma murnar ranar makasassu da bikin Kirismeti. 


An samu sabani yayinda suke kokarin shiga cikin majalisar. Nakasassun wanda adadinsu bai gaza 20 ba sun tubure sai sun shiga kuma haka sukayi duk da jami'in tsaron ya hanasu. An gansu suna suburbudan wani jami'in da yayi kokarin hanasu shiga. Har da yan sandan dake wajen basu tsira ba, yayinda nakasassun suka yaga musu kaya. 




SOURCE: LEGIT.NG


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Daga zanga-zanga, mutane masu nakasa sun nakadawa jami'in tsaro duka a kofar majalisa (Bidiyo) "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?