--
Yanzu yanzu: An kai Shugaba Trump asibiti bayan kamuwa da korona

Yanzu yanzu: An kai Shugaba Trump asibiti bayan kamuwa da korona


Shugaba Donald Trump na Amurka yanzu yana asibitin Walter Reed - An garzaya da shugaban zuwa asibitin ne bayan ya kamu da cutar korona 


Shugabannin kasashe da dama sun aike masa da sakon fatan samun sauki An tafi da Shugaba Donald Trump asibitin sojoji na Walter Reed. 


Hakan na zuwa ne bayan gwajin da aka yi wa shugaban na Amurka ya nuna ya kamu da cutar Covid 19 wato Coronavirus. Asibitin sojojin yana wajen birnin Washington ne kamar yadda Legit.ng ta ruwaito. 


Idan za a iya tunawa Trump da mai dakinsa Melania sun kamu da korona a ranar Alhamis 2 ga watan Oktoba bayan wata hadimar shugaban, Hope Wicks ta kamu da cutar. 


Kafin garzayawa da shi asibitin sojojin, an bawa shugaban na Amurka wasu magunguna. Wannan bayanin na kunshe ne cikin wani sanarwa da likitan shugaban kasar ya fitar kamar yadda CNN ta ruwaito. 


"A halin yanzu Shugaban kasa yana cikin yanayi mai kyau amma akwai gajiya tattare da shi. Wata tawagar kwararru na duba shi kuma tare da su zamu bada shawarar abinda ya dace a masa shi da mai dakinsa," a cewar likitan. 


Shugabanin kasashen duniya da dama sun jajantawa Trump tare da masa fatan samun sauki da shi da mai dakinsa cikinsu har da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya. Rashin lafiyar na shugaba Donald Trump na zuwa ne a lokacin da kasar ta Amurka ke shirye-shiryen yin babban zaben ta a watan Nuwamba. 


A wani rahoton daban, Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Alhamis ya sanar da sakin fursunoni 25, rage wa'adin wasu ciki har da waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa da aka sauya musu zuwa ɗaurin rai da rai. Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin jawabinsa na bikin ranar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴanci. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Yanzu yanzu: An kai Shugaba Trump asibiti bayan kamuwa da korona "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?