--
Kotu ta umurci a ajiye mata basarake mai shekaru 69 a gidan yari a Kogi

Kotu ta umurci a ajiye mata basarake mai shekaru 69 a gidan yari a Kogi


Kotun majistare da ke Lokoja a jihar Kogi ya bada umurnin a bawa wani basarake da wasu mutum 10 masauki a gidan gyaran hali na sati biyu - Hakan na zuwa ne bayan an shigar da karar tuhumar basaraken Momoh Nasir da laifin taimakawa wasu mutane wurin kai wa wasu da ke ibada hari haka sidan 


Ana tuhumar basaraken da sauran mutane 10 da yunkurin aikata kisa, hadin baki wurin aikata laifi, taimakawa wurin laifi da sauransu Wata kotu da ke Lokoja a ranar Juma'a 2 ga watan Oktoba ta bada umurnin ajiye wani mai rike da saurautar gargajiya mai shekaru 69 a karamar hukumar Adavi, Asema Uka (Otumi-Ajoko) Momoh Nasir da wasu mutum 10 a gidan yari kan zargin kisa. 


'Yan sanda suna tuhumar basaraken da wadanda ya hada baki da su da laifin yunkurin kisar kai, hadin baki don aikata laifi, bada taimako wurin aikata laifi wadda ya saba wa wasu sassa na Penal Code a jihar Kogi. 


Alkaliyar kotu, Agatha Shankyula ta bada umurnin a basu masauki a gidan yarin gwamnatin tarayya da ke Koton-Karfe a jihar Kogi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito. 


A yayin da ke bada umurnin, Ms Shankyula ta ce abinda ake zarginsu da aikatawa babban laiffi ne kamar yadda aka bayyana a takardar karar saboda haka akwai bukatar a zurfafa bincike. 


Tunda farko, dan sanda mai shigar da kara Tuesday Ganagana shaidawa kotun cewa wanda ake zargin a ranar 28 ga watan Satumba sun kai wasu mutane hari yayin da suke ibadah a Kabba Junction don zaben kananan hukumomi da za ayi a watan Disamba a jihar. 


Mai shigar da karar ya yi ikirarin cewa wani Momoh Nasiri ya taimaka wa wadanda ake zargin da ke dauke da bindiga, sanda, wuka, duwatsu da adda sun afka wurin da ake ibadan sun raunata mutum takwas. Lauyan wadanda ake tuhumar, Mu'azu Abbas ya roki kotun ta bada belin wadanda ya ke karewa. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Kotu ta umurci a ajiye mata basarake mai shekaru 69 a gidan yari a Kogi "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?