--
Sabbin zafafan hotunan Nafisa Abdullahi kusa da dankareriyar motarta

Sabbin zafafan hotunan Nafisa Abdullahi kusa da dankareriyar motarta


Fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi ta saki wasu zafafan hotunanta - An gano jarumar wacce tauraronta ke ci gaba da haskawa a gaban wata dankareriyar motarta 


A yan baya-bayan nan dai jarumar bata cika fitowa a fina-finan Hausa ba Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nafisa Abdullahi wacce aka fi sani da ‘Sai wata rana’ ta saki wasu sabbin zafafan hotunanta. 


An gano fitacciyar jarumar tsaye a gaban dankareriyar motarta kirar Mercedes-Benz. Nafisa ta saki sabbin hotunan ne a shafinta na Instagram a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoba, sanye da gilashi cikin salo kala-kala. 


Jarumar dai a iya cewa ta yi batan dabo a Kannywood. Sai dai masoyan ta na ci gaba da dakon ganin ta a nan gaba. 


Har ila yau, Nafisa na ci gaba da dukan hankulan masoyan ta a cikin fim ɗin nan na Arewa24 mai dogon zango, 'Labari Na', inda ta ke taka rawa kamar yadda aka tsara. 



View this post on Instagram

Last but not least 🤩🤎 🍫

A post shared by NAFISAT ABDULLAHI (@nafeesat_official) on


A wani labarin kuma, Dino Melaye, tsohon sanata da ya taba wakiltar yankin Kogi na yamma, ya darzo sabuwar motar kirar Lamborghini Aventador Roadstar. Tunde Ednut ne ya wallafa hotuna tare da bidiyon motar alfarmar a shafinsa a ranar Asabar da ta gabata. 


Fitaccen sananne a shafukan sada zumuntar ya wallafa hoton tsohon dan majalisar yana tuka motarsa mai darajar dala miliyan daya wanda yayi daidai da N460,000,000. 


"Sanata Dino Melaye ya siya sabuwar mota kirar Lamborghini Aventandor Roadstar kirar 2020. Kamfanin sun fitar da ita ne a bikin cikarsu shekaru 50. Wannan tana daya daga cikin guda 100 da kamfanin suka yi su a kan dala miliyan 1," 


ya wallafa a Instagram. A watan Maris da ya gabata, tsohon sanatan ya koka da tarin dawainiyar da ke kansa duk da hotunan katafaren gidansa da ya wallafa nasa a kasar ketare. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Sabbin zafafan hotunan Nafisa Abdullahi kusa da dankareriyar motarta "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?