--
Yanzu yanzu: Buhari ya amince a ƙarawa malamai albashi da shekarun aiki

Yanzu yanzu: Buhari ya amince a ƙarawa malamai albashi da shekarun aiki


Shugaba Muhammadu Buhari ya yarda da biyan albashi na musamman ga malaman makaranta - Har ila yau shugaban kasar ya kara wa malaman shekarun aiki daga 35 zuwa 40 


Adamu Adamu, ministan ilimi ne ya sanar da hakan a yau Litinin, 5 ga watan Oktoba Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da biyan albashi na musamman ga malamai. Shugaban kasar ya kuma kara wa’adin shekarun aikin malamai daga shekaru 35 zuwa 40, jaridar This Day ta ruwaito. 


Ministan ilimi, Adamu Adamu, ne ya sanar da hakan a yau Litinin, 5 ga watan Oktoba. Ya bayar da sanarwar ne a cikin wani jawabi na musamman da ya karanto yayinda yake wakiltan shugaban kasar a wajen taron zagayowar ranar malamai ta duniya. Zuwa yanzu dai ba a san yadda tsarin zai kasance ba. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Yanzu yanzu: Buhari ya amince a ƙarawa malamai albashi da shekarun aiki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?