--
Yanda Fusatattun matasa suka kai wa hadimin gwamnan Jigawa hari

Yanda Fusatattun matasa suka kai wa hadimin gwamnan Jigawa hari


Fusatattun matasa sun kai wa hadimin gwamnan jihar Jigawa da ma'aikatan hukumar bada agajin gaggawa na jihar hari 


An kai musu harin ne a hanyarsu ta zuwa Ganuwar Kuka domin duba irin barnar da ambaliyar ruwa ya yi a garin 


Gwamna Badaru Abubakar na jihar ya yi tir da harin inda ya danganta shi da siyasa kuma ya ce Allah ne ya kawo iftila'in don haka ba laifin wani bane Wasu fusatattun matasa a ranar Talata sun kai wa hadimin gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar da wasu jami'an gwamnatin jihar hari.


Channels Television ta ruwaito cewa wadanda aka kai wa harin sune mashawarcin gwamnan na musamman kan ayyukan cigaban garuruwa, Mista Hamza Mohammed da wasu jami'an hukumar bada agajin gaggawa na jihar SEMA. 


An ce sun kai ziyara ne domin duba irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a garin Ganuwar Kuka da ke jihar kafin aka kai musu harin. Wadanda suka kai musu harin sun zo ta sanduna, adduna da wasu makamai masu hatsari domin nuna bacin ransu bisa abinda suka kira tafiyar hawainiya da gwamnatin jihar ke yi game da kai wa wadanda ambaliya ta shafa tallafi da suka ce ya shafi kananan hukumomi 8 karkashin masarautar Hadejia. 


Mashawarcin gwamnan na musamman wadda ya tabbatarwa majiyar Legit.ng da harin ya kara da cewa suna kan hanyarsu na zuwa duba irin barnar da ambaliyar ruwar tayi ne lokacin da fusatattun matasan suka tare su. 


A bangarensa, Gwamna Abubakar ya yi Allah wadai da harin da ya ce yana da alaka da siyasa. "Siyasa ce tasa aka kai harin. Ta yaya za ka kai wa wanda ke kokarin baka tallafi hari? Ba wani bane ya janyo iftila'in.


 "Allah ne ya kaddara kuma ba za mu iya hana faruwar hakan ba. Ko a Amurka ana samun iftila'i. Wanene mu da za mu iya hana abinda Allah ya kaddara ya faru?" in ji shi. 


A wani labarin, Gwamnatin jihar Katsina ta ce makarantun gwamnati da masu zaman kansu na frimare da sakandare za su koma karatu a ranar 5 ga watan Oktoban 2020. Kwamishinan ilimi na jihar Badamasi Lawal ne ya bada wannan sanarwar a ranar Talata a Katsina kamar yadda The Punch ta ruwaito. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Yanda Fusatattun matasa suka kai wa hadimin gwamnan Jigawa hari "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?