--
Tonon asiri: An gurfanar da Baturen Ilimi da ya sace N429,000 daga kudin ciyar da dalibai

Tonon asiri: An gurfanar da Baturen Ilimi da ya sace N429,000 daga kudin ciyar da dalibai




Hukumar EFCC ta cafke Ishaka Abdullahi tare da gurfanar da shi gaban babbar kotun jihar Sokoto, bisa zarginsa da sace N429,000 na ciyar da dalibai 


A cikin shekarar 2019, Hassi Abdullahi, daya daga cikin masu dafa abinci a shirin, ta rasu, sai dai aka ci gaba da tura mata kudi har suka kai N429,000 da Abdullahi ya sace 


Sai dai, Abdullahi, Baturen Ilimi na karamar hukumar Sabon Birni, ya musanya wannan zargi, inda kuma Mai Shari'a Malami Dogondaji ya bayar da belinsa Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta gurfanar da Baturen Ilimi na karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto, Ishaka Abdullahi, bisa zarginsa da sace kudaden shirin ciyar da dalibai. 


An gurfanar da Abdullahi ne a babbar kotun jihar Sokoto, akan zarginsa da aikata laifuka shida da suka hada da karbar kudi ta hanyar yin karya, da suka kai N429,000. 


"Cewar kai Ishaku Abdullahi, a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2018, a karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto, ka cire N135,00 daga asusun Hassi Abdullahi mai lamba 0077129142, bankin Union Plc. 


"Aikata wannan laifi ya ci karo da sashe na 1 (1)(a) na sama da fadi da kudade da kuma sauran dangogin laifuka na dokar 2006, kuma hukuncin laifin na a sashe na 1(3) a cikin dokar." 


Sai dai Abdullahi, ya musanya wannan zargi da ake yi masa, lamarin da ya sa mai shigar da kara, S. H. Sa'ad ya bukaci kotu ta sanya ranar fara shari'a kuma a kaishi ajiya gidan kaso. 


Sai dai, lauya mai kare wanda ake kara, Ibrahim Abdullahi, ya roki kotun da ya bayar da belin wanda ake karar kan cewar yana fuskantar shari'a a kotun kan wani laifi daban. Mai Shari'a Malami Dogondaji, ya bayar da belin wanda ake zargin, kwatankwacin ka'idojin da aka sanya masa a shari'arsa ta baya, inda ya daga shari'ar zuwa ranar 12 ga watan Oktoba, 2020. 


Cikin wata sanarwa daga shugaban sashen watsa labarai na hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya ruwaito cewa sun samu rahoton dakatar da shirin ciyar da dalibai na gwamnatin tarayya. Da suka yi bincike, sai suka gano cewa ana zargin Abdullahi da yin sama da fadi da kudaden ciyar da dalibai na karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto. 


Haka zalika, sun gano cewa, Hassi Abdullahi, wacce ke daya daga cikin masu dafa abinci a shirin, kuma lambar asusu 0077129142, bankin Union Plc., ta rasu a ranar 18 ga watan Maris, 2019. 


Rahotonannin hukumar ya nuna cewa duk da mutuwar matar, ana ci gaba da tura mata kudin abincin daga shirin HGSFP, har su ka kai N429,000, wanda shi Abdullahi ya sace su. Hukumar EFCC ta cafke Ishaka Abdullahi ne bayan da suka kammala bincike. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Tonon asiri: An gurfanar da Baturen Ilimi da ya sace N429,000 daga kudin ciyar da dalibai "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?