LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yadda Za Ku Yi Rijistar Katin Shaidar Zama Dan Kasa


Adaidai lokacin da Najeriya ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen bikin ranar shaidar zama dan kasa ta duniya ranar 16 ga watan Satumba, Hukumar da ke Kula da Shaidar Katin a Najeriya (NIMC) ta ce akalla ‘yan kasar miliyan 42 ne su ka yi rijistar katin.

To sai dai jama’a da daman na ganin adadin ya yi karanci la’akari da yawan mutanen da kasar ke da sun a sama da miliyan 200.

Ana dai bikin wannan ranar ne domin wayar da kan jama’a kan bukatar samun shaida ga dukkan al’ummar duniya.

Rahotanni dai sun nuna akwai akalla mutane sama da biliyan daya da har yanzu ba su da cikakkiyar shaida a hukumance, inda kuma kusan kaso 81 daga cikinsu su ka fito daga yankin Afirka kudu da hamadar Sahara da kuma kudancin nahiyar Asiya.


Ga kadan daga cikin matakan da za ku bi domin mallakar katin shaidar zama dan kasa a Najeriya.


Ga dukkan mai sha’awar yin katin zai ziyarci shafin hukumar da ke https://penrol.nimc.gov.ng/loginForm.tpl.html.php domin cike muhimman bayanai kamar suna, adireshin imel da kuma lambar tsaro ta sirri.

Daga nan in an kammala sai a fitar da takardar shaidar kammalawa a ziyarci ofishin da hukumar ta tanadar domin ci gaba da rijistar.

Za a tafi da wata takardar shaida musamman takardar haihuwa ta Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ko kuma takardar zama dan asalin karamar hukuma ko jiha zuwa ofishin yin rijistar.

A nan kuma za a dauki bayanan mutum kamar tsawo, hoton zanen yatsu da dai sauransu.

Daga nan ne kuma za su baka wata takardar shaida ta wucin gadi kafin katin na ainihin ya fito.


Source: Aminiya Daily Trust 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments