LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Duba Yanda Mutane uku suka mutu sakamakon rushewar wani a gini a Dawanau: Kano


Wani gini ya rushe a unguwar Dawanau, karamar hukumar Dawakin Tofa, sakamakon mamakon ruwan sama A ranar Talata ma wani ginin bene ya rushe a unguwar Gwammaja 'Yan Kosai da ke yankin karamar hukumar Dala a jihar Kano 

Mutane uku ne aka tabbatar da cewa sun rasa ransu yayin da wasu mutanen 8 su ka samu munanan raunku Mutane uku ne su a rasa rayukansu yayin da wani gini ya rushe a garin Dawanau a karamar hukumar hukumar Dawakin Tofa, jihar Kano. 

A cewar jaridar Punch, ginin ya rushe ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a daraen ranar Talata a Kano. Mallam Buba Anwar, mahaifin daya daga cikin wadanda su ka rasu, ya ce ginin ya rushe ne da mialin karfe 03:00 na safiya yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a daren ranar Talata. 

A cewar Anwar, ya ji a jikinsa cewa ginin zai iya rushewa, a saboda haka sai ya umarci matarsa ta kwashe yaransu daga dakinsu. Sai dai, a yayin da iyayen su ka samu nasarar tserar da yarinyarsu, sun rasa yarasnu namiji sakamakon rushewar ginin. 

A wani labarin mai kama da wannan, wani bene ya rushe a sa'o'in farko na ranar Talata inda aka rasa rayukan mutum biyu kuma 'yan gida daya a unguwar Gwammaja 'Yan kosai da ke karamar hukumar Dala. An gano cewa, mutum takwas duk a gida dayan sun samu manyan raunuka bayan sun kasa fitowa daga ginin da ya fadi. 

Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano, Sa'adu Muhammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Vanguard. Ya ce Abdullahi Anas da Abdulmalik Anas sun riga mu gidan gaskiya. 

Muhammed ya ce, "Mun samu kiran gaggawa daga wani Malam Abdullahi Muhammad daga Gwammaja 'yan Kosai a karamar hukumar Dala ta jihar Kano. "Ya kira wurin karfe 1:30 na dare inda ya tabbatar da cewa wani gidan bene ya fadi." 

"Bayan samun kira, mun gaggauta isa da kayan aiki wurin inda muka tara da iyalan a cikin mugun hali. "An mika dukkan wadanda ginin ya fada musu asibitin Murtala Muhammad inda aka tabbatar da mutum biyu sun rasu," a cewarsa. 

A wani labari na daban, masu taimako daga kasar Indiya sun tono wani yaro dan shekara hudu da rai daga cikin burbushin gini da ya danne shi tsawon kwana daya yana karkashi. Mutane sunyi ta murna a ranar Talata 25 ga watan Agusta, bayan an tono yaron daga karkashin ginin da ya danne shi mai hawa biyar. 

Bayan yaron, ginin kuma ya danne mutum 70 a wajen. Lamarin dai ya faru a ranar Litinin 24 ga watan Agusta, a yammacin garin Mahad, dake kudancin Mumbai. 

Sai da aka sanya ma'aikata da yawan gaske da kuma karnuka masu jiyo kamshin abu, inda suka yi ta aiki har zuwa cikin dare suna dauke da bulo da kwanika duka wajen neman wadanda ke da kwana a gaba. 


Source: Legit.gLATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments