--
Rashin Imani: Kotu Ta Daure Mata Kan Nuna Rashin Imani Ga Jariri Mai Kwanaki Goma Da Haihuwa

Rashin Imani: Kotu Ta Daure Mata Kan Nuna Rashin Imani Ga Jariri Mai Kwanaki Goma Da Haihuwa

k


Wata kotun majistare dake zamanta a Dutse babban birnin jihar Jigawa ta umarci a aike da wata mata mai suna Daharatu Muhammad zuwa gidan gyaran hali bisa zargin rashin nuna imani ga wani jariri mai kwanaki 10 da haihuwa.


An dai zargi matar wacce ke zaune a unguwar Jama’are ta karamar hukumar Hadeja bisa da laifukan da su ka hada da nuna rashin imani da kuma halin ko-in-kula ga jaririn.

Tun da farko dai dan sanda mai shigar da kara, Kabiru Warwade ya shaidawa kotun cewa wadda ake zargin ta aikata laifin ne da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Talata, takwas ga watan Satumba.

Ya ce matar dai ta tilastawa jaririn tsotsar gabanta, kuma mahaifiyar jaririn ce ta kamata tana tsaka da aikata danyen aikin.


Kabiru ya ce laifukan sun saba da sassa na 285 da 238 na kundin dokokin penal code.


To sai dai wacce ake zargin ta musanta aikata laifin.


Daga nan ne kuma alkalin kotun, mai shari’a Akilu Isma’il ya dage sauraron karar har zuwa biyar ga watan Oktoba domin ci gaba da sauraron tuhumar.

Source: Aminiya Daily Trust 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Rashin Imani: Kotu Ta Daure Mata Kan Nuna Rashin Imani Ga Jariri Mai Kwanaki Goma Da Haihuwa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?