LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Allah ya isa bamu yafe ba, wannan tsinaniyyar gwamnati ce: Matashin da ƴan bindiga suka kashe mahaifinsa sannan suka sace ƙaninsa a Katsina


Yan bindiga sun kai hari gidan wani ɗan kasuwa, Alhaji Usman Mai Yadi sun kashe shi a daren ranar Litinin - Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da ɗansa mai suna Usman bayan kashe mahaifinsa a garin Yankara da ke Katsina 

Yayan Usman mai suna Younusa Mukhtar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya yi addu'ar Allah ya jikan mahaifinsa ya kuma kubutar da kaninsa Wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun kashe wani Alhaji Mai Yadi sun kuma sace ɗansa, 

Usman a garin Ƴankara da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina. Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin, Kwamared Younusa Mukhtar ya tabbatar da afkuwar hakan a ranar Talata 15 ga watan Satumba ya ce lamarin ya faru misalin ƙarfe 11 na daren ranar Litinin a gidansu. 

"Ta faru ta kare: Ɓarayi sun kashe mahaifi na Alhaji Muntari Mai Yadi sannan sun yi garkuwa da ƙani na Usman," kamar yadda ya rubuta. "Daga Allah mu ke kuma gare shi za mu koma, ɓarayi sun zo gidan mu sun kashe mahaifi na sun tafi da ɗan uwana kuma sun 'amsa waya ta da babur'. 

"Sannan ni kai na da kyar na sha bayan duka na da kan bakin bindiga da kyar na sha bayan na ruga da gudu sauran abubuwan bansan yadda suka faru ba. "Karfe 11:00pm suka shigo babu wani dauki da wani soja ko wani ya kawo mana hakan ya nuna sojojin da aka kawo a Faskari basu da amfani Allah ya isa bamu yafe ba wannan tsinanniyyar gwamnati ce, Allah ya gafartama mahaifina," kamar yadda Yousofu ya rubuta. 

An yi wa wanda ya rasu jana'iza a ranar Talata bisa koyarwar addinin musulunci a gidansa. Kazalika, a daren ranar Lahadi, wasu ƴan bindigan da ba a san ko su wanene ba sun sace mata huɗu ciki har da ƙaramin yaro a lokacin da suka kai hari Ƴankara. Garin Ƴankara yana kan iyakan Katsina da Zamfara ne. 


Tafaru ta kare: Barayi sun kashe mahaifina Alhaji muntari mai yadi sannan sunyi Garkuwa da kanina usman . . Innalillahi...

Posted by Comrd Younusa Mukhtar Yankara on Monday, 14 September 2020


 Source: Legit.gLATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments