--
Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara

Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara


Sojojin saman Najeriya sun yi nasarar lalata wasu gine ginen yan bindiga a dajin Kuyambana da ke jihar Zamfara 

Sojojin sun kai harin ne bayan samun ingantattun bayannan sirri da ke nuna cewa wasu hatsabibin shugabannin yan bindiga na amfani da wuraren a matsayin mafaka 

Sojojin sun yi luguden wuta a gine-ginen tare da kashe yan bindiga da dama da suke cikin gidajen da wadanda suka yi yunkurin tserewa Rundunar sojojin Najeriya ta musamman na Operation Hadarin Daji ta yi nasarar kashe 'yan bindiga da dama sannan ta lalata kayayyakin zirga-zirgansu a wani harin sama da ta kai a dajin Kuyambana da ke Zamfara. 

Sojojin sun kai wannan harin ne a jiya Talata 15 ga watan Satumban shekarar 2020 a cikin hare haren saman da suke kai wa a karkashin atisayen Operation Wutan Daji 2 da aka kaddamar domin kawar da 'yan bindiga da sauran miyagu a yankin Arewa maso Yamma. 

Sojojin sun kai harin ne bayan samun sahihan bayannan sirri da rahotanni tare da amfani da na'urorin leken asiri da suka nuna akwai gidaje da 'yan bindigan ke amfani da su a matsayin mabuya. Kamar yadda bayanan sirrin suka ce, wasu gine ginen da sojojin suka lalata mallakar hatsabiban shugabannin 'yan bindiga 'Sani Mochoko' da 'Damina' ne da suke amfani da su tare da mayakansu. 

Wannan bayannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun hedkwatan tsaro, Manjo Janar John Enenche ya fitar ne a shafin Twitter na rundunar a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba. Jiragen yaki na NAF sun yi ruwan bama-bamai a kan gine ginen inda suka yi wa 'yan bindigan mummunan illa tare da kashe da dama cikinsu.

Sojojin sun kuma yi amfani da jirage masu saukan ungulu sun karasa 'yan bindigan da suka yi yunkurin tsere wa inda suka rika yi musu dauki dai-dai. 

Ga bidiyon yadda aka kai harin a kasa: 



Source: Legit.g


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?