LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yadda 'yan sanda suka azabtar da matashi har ya sheka lahira a Nasarawa


Makusanta wani mutum mai shekaru 27 a jihar Nasarawa sun koka da yadda 'yan sanda suka kashe musu dan uwa  An gano cewa, 'yan sandan sun samu dan uwansa inda suka sanar da shi mutuwar Agbenge amma sun ce basu da hannu a ciki

Bayan duba gawar, an ganta da jini a fuska da kai baya ga kumburin da aka gani a hakarkari da fuskarsa 'Yan uwan wani mutum mai shekaru 37 wanda aka gano ya rasu a hannun 'yan sanda da ke da ofishi a sabuwar Nyanya, Nasarawa, sun zargin 'yan sanda da azabtar da shi har ya mutu. 

Donald Agbenge, wanda aka yi wa ganin karshe a wurin aikinsa a ranar 6 ga watan Satumba a karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, an ga gawarsa a asibitin sabuwar Karu, inda 'yan sanda suka kai gawarsa a sa'o'in farko na ranar Litinin, 7 ga watan Satumba. 

Babban yayan mamacin mai suna Iornumber Agbenge, wanda ya zanta da Aso Chronicle, ya ce sai da ya suma lokacin da 'yan sandan suka sanar masa da cewa kaninsa ya mutum. Kamar yadda yace, a lokacin da ya je ya ga gawar dan uwansa, ya ga jini a fuskarsa da wuyansa, hadi da kumburin da hakarkarinsa da fuskarsa duk suka yi. 

Ya yi bayanin cewa 'yan sandan sun je da motar sintiri suna nemansa a ranar Talata, 8 ga watan Satumba. "Daya daga cikin 'yan sanda ya iso wurin inda ya sanar da ni cewa dan uwana ya mutu a yayin da yake tare da su," yace. Ya jajanta cewa har yanzu 'yan sandan basu bai wa iyalan bayani cikakke na yadda dan uwansu ya mutu ba. 

Ya ce 'yan sanda sun yi ikirarin cewa wani mutum a kusa da wata coci ya kira su inda ya sanar musu da cewa wani mutum na kwance ba a cikin hayyacinsa ba a gaban cocin. "'Yan sanda sun yi ikirarin daukar dan uwana daga cocin, inda suka kai shi asibitin yankin Asokoro da ke Mararaba da kuma FMC Keffi amma duk an ki karbarsa. 

"Sun mayar da shi ofishinsu sannan daga baya suka kai shi asibiti mai zaman kansa. "Amma kuma shugaban asibitin, ya ce lokacin da aka kai dan uwana wurin karfe 3 na daren Litinin, ya riga da ya rasu," yace. A lokacin da aka tuntubi mai gadin cocin, ya ce bashi da masaniya a kan faruwar al'amarin. A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, bai yi martani ga sakonnin WhatsApp da na karta kwana ba da aka dinga tura masa. 


Source: Legit


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments