--
Fursunoni 200 sun tube tsirara kuma suka gudu daga gidan yari a Uganda

Fursunoni 200 sun tube tsirara kuma suka gudu daga gidan yari a Uganda


Jami'an tsaro a Uganda sun bazama neman wasu fursunoni fiye da 200 da suka tsere daga gidan yari, sun shiga wurin ajiye makamai sun tube tufafinsu sannan suka bazama cikin daji a arewa maso gabashin kasar.

A kalla mutane uku - daya soja biyu kuma cikin fursunonin - sun mutu yayin musayar wuta da aka yi a cewar kakakin rundunar sojin kasar, Birgediya Flavia Byekwaso. Fursunonin sun tsere daga gidan yarin ne a ranar Laraba kusa da barikin sojoji da ke Moroto.

"Sun ci galaba a kan direbobin da ke aiki a ranar," in ji Byekwaso. Fursunonin da suke tsere rukakun masu laifi ne da aka daure saboda laifuka masu alaka da satar shanu a yankin, a cewar ta.

Sun tube tufafinsu domin kada a yi saurin gane su da lauyin ruwan dorowa na kayan gidan yarin sannan suka tsere wurin Dutsen Moroto, wani gari mara mutane sosai a cewar kakakin sojin.

"Har yanzu muna cigaba da nemansu," in ji ta, a lokacin da ta ke yi wa mutane gargadin cewa za su iya afkawa gidajen mutane don neman tufafin da za su saka. Kokarin da aka yi na ji ta bakin hukumomin gidan yarin bai yi wu ba a lokacin hada wannan rahoton kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Sun kai sumammen ne a garin Adu da ke Chanchanji a ƙaramar hukumar Takum da ke jihar Taraba.


Source: Legit 



LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Fursunoni 200 sun tube tsirara kuma suka gudu daga gidan yari a Uganda"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?