--
Hamshakin mai kudi a duniya ya cimma burinshi na zama talaka kafin ya mutu, duba abinda ya yi

Hamshakin mai kudi a duniya ya cimma burinshi na zama talaka kafin ya mutu, duba abinda ya yi


Biloniyan dan kasuwa Charles Chuck Feeney a karshe dai ya talauce bayan ya bayar da duka dukiyar shi sadaka tun yana raye. Mutumin wanda ya samar da kamfanin Duty Free Shoppers, ya ce akwai dadi sosai idan ka bayar da dukiyar ka tun kana raye ba wai sai ka mutu ba. A wani rahoto da Forbes ta fitar, sama da shekaru arba'in, Feeney ya sadaukar da sama da dala biliyan takwas, sama da naira tiriliyan uku kenan a kudin Najeriya.



Ya bayyanawa Forbes cewa: "Mun koyi darasi da yawa. Zamu yi abu da yasha bamban, amma naji dadi sosai. Naji dadi dana nayi wannan abu tun ina raye." Feeney ya nuna jin dadin shi ga mutanen da suka goyi bayan shi wajen bayar da duka abubuwan da ya mallaka. Inda yake rokar sauran mutane suyi koyi da shi.



Ya ce: "Godiya ta ga wadanda suka goyi bayana da kuma wadanda suke tunanin bayarwa tun suna raye: Ku gwada zaku so hakan." Yariman Dubai mai jiran Gado, Sheikh Hamdan bin Mohammed bin Rasha Al-Maktoum, ya nunawa duniya cewa ba komai bane idan ka zama mai adalci ga dabbobi. Yariman ya daina amfani da wannan mota domin ya tabbatar da lafiyar wadannan tsuntsaye.


Source: Legit


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Hamshakin mai kudi a duniya ya cimma burinshi na zama talaka kafin ya mutu, duba abinda ya yi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?