LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Boko Haram: Dahiru Bauchi, ya musanta goyon bayan Mailafia a kan ikirarinsaFitaccen Malami Sheikh Dahiru Bauchi, ya tsame kansa daga ikirarin da ke fitowa daga Mailafia na cewa yana goyon bayansa Bayan kwashe sa'o'i a ofishin hukumar DSS a karo na uku, Mailafia ya ce fitattun jama'a a kasar nan har da shehin malamin suna goyon bayan ikirarinsa 

Sai dai Malamin ya ce ko jaje bai taba hada shi da Mailafia ba balle ya goyi bayan cewa gwamnan arewa ne kwamandan Boko Haram Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a ranar Laraba ya musanta goyon bayan ikirarin tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafia, wanda yace wani gwamnan arewa shine kwamandan Boko Haram. 

A wata tattaunawa da Malamin yayi da jaridar Daily Trust a ranar laraba, Dahiru Bauchi mai shekaru 93, ya ce bai tura sakon goyon baya ko jaje ga Mailafia ba ko bayan da yayi hira da wani gidan rediyo a kan kashe-kashen kudancin Kaduna da kuma Boko Haram. 

Sau uku hukumar tsaro ta fararen kaya ta gayyaci Mailafia domin amsa tambayoyi a ofishinta da ke jihar Filato. A yayin zuwansa na karshe a ranar Litinin, 14 ga watan Satumban 2020, bayan tauuanawa da jami'an tsaron na farin kaya, Mailafia ya sanar da malamai, lauyoyi da 'yan jaridu cewa, fitattun jama'a a kasar nan suna goyon bayansa. 

"Na samu sako daga manyan malaman addinin Islama da suka hada da Sheikh Dahiru Bauchi. "Ya turo min sakon inda yake bayyana cewa yana yi min addu'a," Mailafia yace yayin tattaunawa. "Matasan Musulmi suna goyon bayana. Suna yi min addu'a. Sun yadda cewa ni ne muryarsu, hakazalika matasan Kiristoci," yace. 

Amma kuma, Sheikh Dahiru Bauchi, wanda yake daya daga cikin manyan jiga-jigan darikar Tijjaniya wanda ke da miliyoyin mabiya a Najeriya da sauran sassan duniya, ya ce bai yi magana da kowa ba, kuma bai aike kowa wurin Mailafia ba. 

"Idan dai Mailafia ne wanda ya yi mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya lokacin da Sanusi Lamido Sanusi yake gwamnan, tabbas na yi musu addu'ar nasara a lokacin suna bankin, kuma saboda Sanusi ne," tsohon yace bayan kallon bidiyon tattaunawa da Mailafia. "Amma kuma ikirarinsa da zarginsa a kan gwamnonin arewa, bana tare da shi kuma ban aika wani wurinsa ba," yace.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi addu'ar zaman lafiya da daidaituwa a Najeriya, kuma ya shawarci Musulmi da su nemi yafiyar Allah da kuma daidaituwar kasar nan. 

Source: Legit


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments