LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Rikicin aure: Mun daidaita tsakanina da Muhammad Babangida, 'yar gidan biloniya, Rahma Indimi

Diyar fitaccen mai kudi Rahma Indimi ta bayyana cewa ta daidaita da tsohon mijinta

Ta bayyana hakane bayan wani rubutu da aka yi a kanta a shafukan sadarwa

Sai dai har yanzu ance akwai sauran rikici dake tsakaninsu a kotu kan yaransu Rahama Indimi ta bayyana cewa ta daidaita da tsohon mijinta, Muhammed Babangida.

A shekarar 2016, labarai sun yadu cewa auren su da suka shafe shekaru 14 suna tare, tsakanin 'yar gidan fitaccen mai kudin nan Mohammed Indimi, da Muhammed dan gidan tsohon shugaban kasar mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya rabu.

Duka su biyun sunyi ta shiga kotu tun lokacin kan rikicin wanda zai rike yaran.

Sai dai kuma a lokacin bikin Sallah babba da aka gabatar a watan Yuli, 2020, Rahma taje gidan Ibrahim Babangida, inda 'ya'yanta da kuma 'ya'yan matar tsohon mijinta, Umma, suka dauki hoto da kakansu.

Rahma ta wallafa wannan hoto a shafinta na Instagram, inda wani shafin yada labarai na yanar gizo ya bayyana cewa ta yanke hoton 'ya'yan Umma kafin ta wallafa hoton.

Da take martani akan wannan rubutu, Rahma tayi watsi da zargin, inda kuma ta bayyana cewa ita da tsohon mijin nata tuni sun daidaita.

"Daga yaya wannan ya zama labari ma kaiiii, za abi kowacce hanya ayi kudi, da farko akwai uku daga cikin 'ya'yana a hoton ba biyu ba, na biyu bani da hurumin da zan wallafa hotunan 'ya'yan matar tsohon mijina, haka kuma Muhammed ya bayyana mini banda sanya hoto a shafukan sadarwa.

Ni da Muhammed tuni mun daidaita mun koma zaman lafiya, saboda haka ku daina irin wannan shirmen."

cewar rubtun da ta wallafa. Jaridar Linda Ikeji ta ruwaito cewa tun a shekarar data gabata ne dai Muhammed da Rahma suka daidaita, kuma suna tattaunawa su gani ko zasu koma su cigaba da zaman aure. Duk da dai har yanzu ana kotu kan maganar 'ya'yan nasu, nan da mako biyu za a koma kotu don cigaba da shari'a.


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


Post a comment

0 Comments